Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
A wani mataki na bunƙasa ilimi da cigaban fasahar zamani, shugaban ƙaramar hukumar Katsina, Hon. Isah Miqdad AD Saude, ya bayyana shirin gina cibiyar koyon kimiyyar sadarwa ta zamani (Digital Learning Centre) a makarantar firamare ta Layout, Wakilin Kudu II.
Da zarar an kammala aikin, cibiyar za ta kasance cikin na’urorin kwamfuta na zamani da kayan aikin ICT, wadda za ta zama cibiyar koyon fasahar kwamfuta da dabarun dijital da kuma koyo ta yanar gizo.
Domin tabbatar da ci gaba da aiki ba tare da tangarɗa ba shugaban ƙaramar hukumar ya ce za a samar da wutar lantarki mai aiki na awa 24 a rana, domin bayar da yanayi mai kyau da dacewa ga masu koyo da bincike.
Wannan shirin na Hon. Miqdad shi ne na farko da wata ƙaramar hukuma ta mayar samar na koyon ƙirkire-ƙirkire, ilimi da ci gaban fasahar zamani, tare da bin diddigin manufofin jihar Katsina na cigaban dijital da gina jarin ɗan Adam.
Kwanan baya ne shugaban ƙaramar hukumar ya sami lambar yabo daga fadar shugaban ƙasa kan maida aikace-aikacen ƙaramar hukumar zuwa dijital.
