Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Majalisar dokokin kano ta fara yunƙurin samar da wata doka wadda za ta tilasta yin amfani da harshen uwa musamman harshen Hausa a matsayin hanyar koyarwa a makarantun jihar, domin bunƙasa fannin ilimi.
Hakan ya biyo bayan kuɗurin da ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Takai a zauren Dr. Musa Ali Kachako ya gabatar.
Da yake ƙarin bayani a gaban majalisar, Dr. Kachako yace samar da dokar zai dace da yadda tsarin koyarwa yake a duniya kamar yadda ƙasashen da suka ci gaba irin su China, Japan da India suka samu babbar nasara ta hanyar yin amfani da harshen uwa wajen koyarwa a makarantun su.
Kazalika, Dr. Kachako ya ƙara da cewa rungumar harshen uwa a matsayin hanyar koyar da ɗalibai zai ƙarawa dalibai fahimta da san karatu da rage yawan faɗuwa jarrabawa da ake samu, haka kuma zai taimakawa ɗorewar al’adu da haɗe kan al’umma.
Wakilin Blueprint Manhaja a Kano ya rawaito cewar, bayan doguwar mahawara a zauren, majalisar ta miƙa ƙudurin zuwa kwamitin ta na ilimi domin yi masa tatsa da tsifa kuma ya bawa majalisar shawarar ɗaukar mataki na gaba.
