
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kwamishinan ƴan sanda a Jihar Legas, Olohundare Jimoh, ya jaddada aniyarsu ta cigaba da ayyana ɗan gwagwarmaya Omoyele Sowore a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo, yana mai alwashin cewa za su bi dukkan hanyoyin da doka ta tanada wajen ganin sun kama shi.
A ranar Litinin ne kwamishinan ya sanar da ayyana Sowore a matsayin wanda suke nema bisa zargin sa da ta da zaune-tsaye acikin jama’a sakamakon jagorantar wani gangami da ya haddasa cinkoson ababen hawa a yankin Third Mainland Bridge da ke jihar.
Da yake magana a wata hira da gidan talabijin na Sunrise Daily, Kwamishina Jimoh ya ce har yanzu Sowore bai kai kansa offishin ƴan sanda ba tun daga lokacin da aka sanar da batun nemansa, lamarin da ya sa suke cigaba da farautar sa.
Ya ce, lallai za su cigaba da bibiyarsa har sai ya shiga hannunsu ta yadda doka za ta yi aiki a kansa.
Ya bayyana cewa, lauyan ɗan gwagwarmayar ya tattauna da shi da saƙon kar ta kwana a ranar Litinin ɗin a lokacin da yake magana akan wani tashin-tashina, sannan ya kuma aike wa jami’in da ke kula da lamuran shari’a na ƴan sanda domin cigaba da bibiya.
Kazalika, Jimoh ya ce yana da ƴancin ayyana Sowore a matsayin wanda ake nema ruwa-a-jallo da kuma ƙalubalantar duk wanda ya nemi ja da shi akan haka a kotu.
Haka kuma, Kwamishinan ya yi watsi da ikirarin Sowore na cewa Sufeto Janar na ƴan sanda, Kayode Egbetokun ya umarci a harbe shi da zarar an gan shi, yana mai bayyana hakan a matsayin zance mara tushe da aka ƙirƙira da nufin ruɗar da al’umma.
