Ƙaramar Hukumar Sabon Birni ta zama kamar shalkwatar ‘yan ta’adda a Nijeriya

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rahotanni daga Jihar Sakkwato a Arewa maso Yammacin Nijeriya, na cewa ‘yan bindiga a yankin Sabon Birni na ci gaba da satar jama’a masu ɗimbin yawa tare da kashe wasu.

Bayanan sun ce ‘yan fashin dajin na ci gaba da rike aƙalla mutum 150 baya ga karin wasu ashirin da takwas da aka sace a ƙarshen makon nan a ƙuuyen Makuwana da ke ƙaramar Hukumar Sabon Birnin.

Wannan na zuwa ne ƙasa da mako guda da wasu masu garkuwa da mutane suka kashe Sarkin Gobir na Gatawa, Alhaji Isa Muhammad Bawa.

Lamarin ya faru kwanaki bayan da wasu ‘yan bindiga da suka yi garkuwa da sarkin da ɗansa da wasu ƙarin mutum shida a hanyarsu ta zuwa birnin Sakkwato.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC cewa suna cikin wani yanayi na zaman zulumi:

‘’Ba bu ranar da ‘yan bindiga ba su shigowa ƙauyuka, sansanonin da a garesu kewayen ƙauyukan suna ɗaukar jama’a, ainihin ranar da aka yi sanarwar ba bu ran sarki, daddaren nan sai da suka shiga ƙauyen ‘yan Haru mai nisan kilomita biyu da sabon birni inda suka ɗauki mutum fiye 20 bayan mutum fiye da 10 da suka yi garkuwa da su”, in ji shi.

Mutumin ya ce mazauna garuruwan Tsammaye da ungwar Lalle su na shirin tashi ya kuma yi ikirrain cewa ba bu wani ‘mataki da mahukuntan suka ɗauka.’

Sauran wuraren da maharan suka addaba a sabon birnin sun haɗa da Kwanar Maharba da Tursawa da sauransu.

Sanata Ibrahim Lamido wanda ɗan majalisar dattawan Nijeriya ne mai wakiltar Sakkwato ta Gabas ya shaida wa BBC cewa akwai gaskiya a cikin al’amarin:

”Wannan abu da ka ke ji gaskiya ce, har yanzu ‘yan ta’adda suna nan a ƙauyukan Sabon Birni suna ta ta’addanci, suna ɗaukar mutane, suna kai su daji suna garkuwa da su.”

Sanatan ya ce ”ƙaramar hukumar sabon birni ta zama kamar helkwatar ‘yan ta’ada ba wai in ce maka Sakkwato kawai, a Nijeriya kullum ta’addanci ake yi musu.’

‘’Ina gaya maka garuruwan sabon Birnin da ke da wannan matsala sun kai tara a halin yanzu,’’ in ji shi.

A wani labarin kuma ƙungiyar ci gaban gobirawa ta duniya ta yi kira ga gwamnati da ta taimaka masu wajen ganin an anso gawar Sarkin na Gobir na Gatawa daga hannun ‘yan bindiga.

Shugaban ƙungiyar Ibrahim Alhassan Sabon Birni ya ce su na son kamar yadda ake yi wa kowane Musulmi sutura shi ma Sarkin suna so a yi masa haka, inda ya ƙara da cewa rashin samun gawar ya sanya su cikin tashin hankali.

By ukarofi