Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Shugabannin ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa (NANS) sun ce a shirye suke su gana da shugaban ƙasa Bola Tinubu idan buƙatuwar hakan ta taso, kan buƙatarsu ta ganin an warware matsalar ƙarin farashin man fetur.
Sakataren ƙungiyar, Daɓid Bariereka ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a garin Fatakwal na Jihar Ribas.
A cewarsa, a halin yanzu ƙungiyar ɗaliban na tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar man fetur da suka haɗa da hamshaƙin ɗan kasuwa Aliko Dangote, da ‘yan kasuwar man fetur, da ƙaramin ministan man fetur, domin lalubo hanyar magance matsalolin da jama’a ke fuskanta.
Wannan ci gaban na zuwa ne bayan aungiyar zaliban ta dage kan ci gaba da gudanar da zanga-zangar adawa da ƙarin farashin man fetur a faɗin ƙasar.
Tun da farko ƙungiyar ta sanya ranar 15 ga Satumba, 2024, don yajin aikin na ƙasa baki ɗaya.
Shugaban Majalisar NANS, Henry Okuomo a lokacin da ya bayyana a matsayin baƙo a gidan Talabijin na Channels Teleɓision’s Sunrise Daily ranar Juma’ar da ta gabata, ya ce ƙungiyar na da ƙarfin riƙe gwamnati saboda ba ta jin daɗin halin ƙuncin da ƙasar nan ke ciki.
A ɗaga ɓangaren kuma, dangane da aarin farashin man fetur da aka yi a baya-bayan nan, ƙungiyar ta NANS ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta ƙara rancen ɗalibai daga naira 20,000 zuwa N40,000 domin rage matsalolin kuɗi da ɗalibai ke fuskanta.
Shugaban Majalisar NANS, Babatunde Akinteye ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Abuja ranar Litinin, inda ya jaddada buƙatar gwamnati ta sa baki don taimaka wa ɗalibai wajen tafiyar da tsadar rayuwa ba tare da tauye musu iliminsu ba.
Akinteye ya bayyana cewa ƙarin da ake shirin yi yana da matuƙar muhimmanci don tabbatar da cewa dalibai ba su yi wa ɗalibai nauyi a lokacin da suke neman ilimi ba. Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta rage yawan kuɗaɗen da take kashewa, yana mai cewa a lokacin da ake neman ‘yan Nijeriya su sadaukar da kansu, ya kamata masu riƙe da madafun iko su yi koyi da su.
A nasa jawabin, Akinteye ya buƙaci kwantar da hankali da haƙuri, yana mai tabbatar da cewa sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta ɓullo da shi zai haifar da sakamako mai kyau.
