Ƙaruwar satar yara: Barazana ga makomar ƙasa

Spread the love

A cikin ‘yan watannin da suka gabata, rahotanni masu tayar da hankali sun ƙara bayyana gaskiyar da ke damun ƙasarmu — ƙaruwar satar ƙananan yara a sassa daban-daban na Nijeriya, musamman Arewacin ƙasar. Wannan al’amari mai matuƙar muni yana ƙara zama abin damuwa ga iyaye, malamai da hukumomi, musamman ganin yadda masu aikata irin wannan laifi ke ƙara dabaru da ƙwarewa wajen ɓata wa al’umma rai da rusa kwanciyar hankali.

Rahotannin hukumomin tsaro da jaridu sun tabbatar da cewa satar yara yanzu ba ta taƙaita ga manyan birane kamar Abuja, Legas, Kano, da Fatakwal ba. Ko a ƙauyuka, an fara samun rahotannin yara da ake ɗauka cikin dabara — wasu ana sayar da su, wasu ana amfani da su wajen bara, wasu kuma ana kai su wasu jihohi ko ƙasashen waje domin bautar da su. Wannan na nuni da cewa matsalar ta zama babbar barazana ga lafiyar al’umma da makomar ƙasar gaba ɗaya.

A wannan yanayi, abu ne da ya dace mu yaba wa Hukumar Yaƙi da Safarar Mutane ta NAPTIP saboda irin gagarumar rawar da take takawa wajen daƙile wannan annoba. NAPTIP ta daɗe tana fafutukar yaƙi da safarar mutane da kuma satar yara, ta hanyar haɗin gwiwa da hukumomin tsaro, ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, da kuma jama’a a matakan gari da ƙasa. Duk da ƙalubalen da take fuskanta — kamar ƙarancin kayan aiki, ƙarancin ma’aikata, da buƙatar haɗin kan jama’a — hukumar ta nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen ceto rayukan yara da dama.

Duk da haka, yakamata gwamnati da al’umma su fahimci cewa yaƙi da satar yara ba na NAPTIP kaɗai ba ne. Wannan yaƙi ne da ke buƙatar haɗin kan duka matakai na gwamnati da jama’a. Yara su ne gajiyayyun ɓangarori na al’umma, kuma kariya gare su kariya ce ga makomar ƙasa. Duk lokacin da yara ke cikin barazana, makomar ƙasa na cikin haɗari.

Abin takaici ne yadda wasu iyaye ke nuna sakaci wajen kula da yaransu. A wasu lokuta, yara kan tafi makaranta ko kasuwa ba tare da kulawa ba, wasu kuma ana barinsu cikin gidaje ko unguwanni ba tare da wani tsaro ba. Haka kuma, akwai matsalar talauci da rashin ilimi, waɗanda ke jefa wasu cikin jaraba ta sayar da yara ko karɓar tayin aikin da ba su san asalinsa ba.

NAPTIP ta yi nasarar gano irin waɗannan hanyoyin, inda ta kafa tsare-tsare na wayar da kai ta hanyar shirye-shiryen rediyo da talabijin, tarukan ilimantarwa, da kuma amfani da kafafen sada zumunta don faɗakar da iyaye da malamai. Haka kuma, hukumar na aiki tare da majalisun jihohi wajen samar da dokoki da ke ƙarfafa hukunta masu aikata laifin satar yara da safarar mutane.

Gwamnati, musamman ta tarayya, ta kamata ta ƙara tallafa wa hukumar ta fuskar kuɗi da kayan aiki. Wajibi ne a tabbatar cewa NAPTIP ta samu cikakken damar gudanar da bincike cikin ƙwarewa tare da saurin hukunta masu hannu a cikin laifukan. Wannan ya haɗa da samar da motocin sintiri, kayan fasaha na bincike, da ingantattun cibiyoyin kula da waɗanda aka ceto.

A gefe guda kuma, dole ne a duba rawar da cibiyoyin addini da al’umma ke takawa. Limamai da malamai su riƙa jan hankalin jama’a kan illolin satar yara da safarar mutane. Ya kamata a dawo da darussan tarbiyya a makarantu, tare da koyar da yara hanyoyin kare kansu da sanin abin da ya dace su gujewa.

Haka kuma, akwai buƙatar a ƙara tsaurara matakan tsaro a wuraren da yara ke taruwa — makarantu, kasuwanni, cibiyoyin kiwon lafiya da wuraren ibada. Yakamata jami’an tsaro su riƙa lura da masu motsi da yara ba tare da hujja ba, musamman a manyan titi da tashoshin mota.

A lokaci guda, ya kamata gwamnati ta kalli matsalar da idon basira: yawancin masu aikata irin wannan laifi ba sa yin haka don nishaɗi, sai don ribar da suke samu daga wasu manyan ƙososhi da ke cikin ɓoyayyun ƙungiyoyi. Don haka, ya zama wajibi a bi waɗannan ƙososhi da matakan bincike na zamani, a kamo su, a gurfanar da su a kotu, sannan a tabbatar da hukunci mai tsanani da zai zama izina ga wasu.

NAPTIP ta riga ta yi kyakkyawan tasiri wajen rushe wasu irin waɗannan ƙungiyoyi a jihohin Edo, Anambra, Kano da Filato, inda ta ceto mata da yara da dama daga hannun masu safarar mutane. Irin wannan nasara na nuna cewa da tallafi da haɗin kai daga gwamnati da jama’a, za a iya cin ma nasara ta gaskiya.

Haka kuma, ya kamata gwamnati ta ƙarfafa haɗɗn kai tsakanin NAPTIP da Hukumar Shige da Fice, NSCDC, DSS, da ‘yan sanda, domin a samu daidaito wajen musayar bayanai da gudanar da bincike cikin sauri. Satar yara tana buƙatar dabaru na zamani — amfani da fasahar gano mutum (biometrics), na’urorin CCTV, da tsarin rajistar yara daga haihuwa.

A ƙarshe, ya kamata mu gane cewa yaƙi da satar yara ba ya buƙatar makamai kawai — yana buƙatar haɗin kai, tausayi, da wayar da kai. Kowa da kowa yana da rawar da zai taka — daga iyaye, malamai, shugabanni, da jami’an tsaro har zuwa gwamnati da ƙungiyoyin farar hula.

NAPTIP ta zama abin koyi a wannan yaƙi, ta hanyar jajircewa, gaskiya da aiki tuƙuru. Ya dace gwamnati ta ƙara tallafa mata, domin wannan hukumar ce ginshiƙin kare martabar yara da mutuncin al’umma. A lokacin da satar yara ke ƙaruwa, muna da tabbacin cewa da haɗin kai da cikakken goyon bayan jama’a, za mu iya tabbatar da cewa Nijeriya ta koma ƙasa mai tsaro da adalci, inda yara za su tashi cikin kariya da ’yanci.

By ukarofi