Ƙasurgumin ɗan Boko Haram ya miƙa wuya ga sojojin Nijeriya

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar dakarun ƙasashen da ke yaƙi da ƙungiyar Boko Haram ta MNJTF, ta ce wani ƙasurgumin ɗan Boko Haram, mai suna Bochu Abacha, ya miƙa wuya ga sojojin Nijeriya da ke aiki a ƙaramar hukumar Kukawa na jihar Borno.

Jami’in yaɗa labarai na rundunar a Ndjamena, Laftanar Kanar Olaniyi Osaba ne ya bayyana haka ga manema labarai a Maidguri ranar Asabar.

Osaba ya ce Abacha, wanda ya kasance yana da hannu a kai hare-hare da dama, ya amsa shiga gaba wajen kai hare-hare a kan hanyar Mongunu zuwa Baga.

“Abacha ya miƙa wuya ne sakamakon zafafan farmaki da MNJTF ke kai wa da kuma buƙatarsa ta son ganin an samu zaman lafiya,” inji Osaba kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya ruwaito.

Ya ce ɗan Boko Haram ɗin ya kuma miƙa bindiga AK 47 ɗaya cike da harsasai da wayar salula da layin wayar kamfanin Airtel da kuma kuɗi N32,500.

Jami’in ya ce wanda ake zargin na bai wa hukumomi bayan sirri da zai taimaka musu a aiki.

A ɗaya gefen, rundunar MNJTF tare da haɗin gwiwar wasu jami’ai sun yi wasu mayaƙan Boko Haram kwantan ɓauna tare da kashe ɗaya daga cikinsu.

Dakarun sun yi artabu da mayaƙan, inda daga bisani wasu suka samu damar tserewa har da barin makamansu.

Osaba ya ce sun gano motoci uku ɗauke da kayan abinci da sauransu.

By ukarofi