Rundunar sojin Nijeriya ta gina ajijuwa kyauta a makarantar Kano

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar Sojin Nijeriya ta gina ajijuwa kyauta a makarantar sakandaren Datti Ahmed dake ƙauyen Wurure dake ƙaramar Hukumar Gwale a jihar Kano.

Rundunar a ƙarƙashin shugabancin Babban Hafsan Sojoji Taoreed Lagbaja ta kuma gyara ginin ofisoshi tare da samar da kujeru da tebura 216 a makarantar.

Lagbaja yayin da yake damƙa ajijuwan da rundunar ta gina ranar Asabar ya ce rundunar ta yi haka ne domin ƙara wa iyaye da yara ƙarfin guiwar maida hankali wajen karatunsu.

Lagbaja ya gode wa Shugaban ƙasa Bola Tinubu kan goyan bayan da yake bai sojojin Nijeriya sannan ya yi alƙawarin cigaba da yin biyayya ga shugaban ƙasa.

Bayan haka shugaban ayyuka na ginin Sani Bashir ya ce rundunar ta gudanar da wannan aiki ne domin ƙara wa mutanen garin ƙarfin guiwar maida hankali wajen tura ‘ya’yan su makaranta.

By ukarofi