Ƙauyanci ne Bahaushe ya riƙa magana da ɗansa da Turanci – Hon. Mukhtar Madobi

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano 

An bayyana cewa ƙauyanci ne da gidadanci da kuma rashin sanin ciwon kai da rashin darajar harshe ya sa mutum Bahaushe zai riƙa magana da ƙaramin yaronsa da Turanci don kawai yaron nan wai ya taso da jin Turanci, wanda kuma Turanci daban ilimi daban.

Turanci harshe ne wanda ko ba ka je makaranta ba za ka iya, kamar yadda ɗan majalisar dokoki mai wakiltar ƙaramar hukumar Madobi a majalisar dokokin Jihar Kano kuma shugaban kwamitin ilimi na majalisar dokokin, Hon Mukhatar Sulaiman Madobi ya bayyan a hira da manema labarai kan ranar Hausa ta Duniya da aka yi.

Haka kuma ya ce kasancewar Kano ce cibiyar harshen Hausa ta duniya kamar yadda ake cewa jalla babbar Hausa yaro ko da me ka zo an fi ka, wannan ya nuna shaharar Hausa da Kano ta yi don haka akwai buƙatar a tilastawa baƙin haure koyon harshen Hausa kafin mu yi hulɗa da su ta ilimi da makamantansu domin kowanemu da ya fita ƙasashen waje irinsu Rasha, China, Indiya, Sudan da sauransu sai an tilasta ma ka koyi harshensu kafin ka fara karatu a ƙasar, kuma wannan ce ta sa ƙoƙarinmu na gayran tsarin ilimin jihar Kano a majalisar dokoki wanda ake kan tsohon tsari tun 1960 mun yi la’akari da matsayin da Hausa da za ta samu ƙarin ƙarfi a sabon tsarin ilimin Kano mai zuwa ba da da ɗewaba, kamar yadda Hon. Sulaiman Mukthar ɗan majalisar mai wakiltar ƙaramar Hukumar Madobi ya bayyana.

Har ila yau ya bayyana cewa harshen Hausa harshe ne mai daraja kuma abin alfahari ne ga duk wani Bahaushe na asali, kamar ko wane harshe ilimi daban Turanci daban in ma da wani harshe da ya fi Hausa daraja to sai dai ace shi ne harshen larabci domin shi ne harshe shugaban mu ma’aikin Allah

Shi ma ɗaya daga cikin masana da ya gabatar da jawabi a wani taro mai alaƙa da bunƙasa Hausa wato Dakta Maigida Kachako ya ce a Hausa akwai ƙwararru masu karɓar haihuwa da ake kira ingozoma a rayuwar Hausawa, wanda su ke gane jariri mahaukaci ne, ko mai hankali, kurma ne, ko .akaho ne, tun ranar da aka haife jariri, amma yanzu an barwa asibiti komai saboda rashin sanin hakiƙanin tsarin rayuwar Hausawa na asali.

Tun da farko a jawabinta shugabar taron ranar Hausa ta duniya,  Farfesa Maryam Mansur Yola, ta ce Hausawa ne saboda suntashi cikin Hausa, su ke ganin arhar Hausa amma harshe ne mai tsada, mai daraja, mai cike da tsari, da surika, na samar da rayuwar ɗan adam mai ingantance, wanda yanzu haka akwai mutane sama da miliyan 500 da ke Magana da harshen Hausa a duniya.  

By ukarofi