Daga RABIU SANUSI a Kano
Shugaban ƙaramar Hukumar Katsina, Hon. Isah Miqdad AD Saude, ya jagoranci wata tawaga ta musamman domin gudanar da ziyarar gani da ido a wasu yankuna da ake hasashen ambaliyar ruwa da zaizayewar ƙasa ka iya shafa.
Ziyarar wadda ta kasance wani mataki na gaggawa da nufin tantance halin da ake ciki kai tsaye, tare da gano hanyoyin da suka dace na ɗaukar matakan kariya na nan take da na dogon lokaci domin kare rayuka, dukiyoyi da kuma bunƙasa tattalin arzikin al’ummomin da abin ya shafa.
Wasu daga cikin Unguwannin da aka ziyarta sun haɗa da Masoya Annabi ƙuarters da ke kan hanyar Batsari a cikin mazabar Wakilin Yamma II, Rahamawa ‘Yar Yara a Wakilin Kudu III, Mani House a Wakilin Kudu II, Shinkafi da Gezawa a Shinkafi A, Kwado a Shinkafi B, da kuma yankin bayan Sakatariyar Karamar Hukumar Katsina da ke cikin mazabar Wakilin Gabas I.
A cikin tawagar da ta raka shugaban akwai Sakataren Karamar Hukumar Katsina, Daraktan Sashen Ayyuka, Shugaban Majalisar Kansiloli wanda shi ma Kansila ne na Shinkafi B, tare da kansilolin Wakilin Yamma II, Wakilin Gabas I da Wakilin Kudu III.
Yayin tattaunawa da al’ummar yankunan, Hon. Miƙdad ya tabbatar da cewa gwamnatin Karamar Hukumar za ta ɗauki matakan da suka dace tare da isar da rahoton ƙorafe-ƙorafen jama’a zuwa ga hukumomin da abin ya shafa.
Ya jaddada cewa ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen fuskantar ƙalubalen muhalli, domin kare lafiyar al’umma, tsaron dukiyoyinsu da kuma tabbatar da zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki a cikin ƙaramar hukumar.
