Ƙudirin zangon shekara shida ga shugaban ƙasa da gwamnoni ya tsallake karatun farko a majalisa

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Majalisar wakilai ta gudanar da karatun farko ga ƙudirin da ke neman kwaskwarima ga kundin 1999 wanda zai mayar da yin shekara shida a kowane zango na ofishin shugaban ƙasa da gwamnoni da shugabannin ƙananan hukumomi.

Ofishin shugaban ƙasa da na gwamnoni ya tsallake karatun ne a yayin zaman majalisar na ranar Laraba wanda Ikenga Ugochinyere da ke wakiltar mazaɓar Ideato ta Kudu da ta Arewa ta jihar Imo ya gabatar tare da wasu ƴan majalisa 50.

Haka nan, ƙudirin na neman goyon bayan sakin layuka na 7, 135, 137, 180 da kuma na 182 kamar yadda ya ke a kundin shekarar 1999.Jumla ta biyu na ƙudirin na neman kwaskwarima ga sakin layi na 7 ta hanyar sanya reshe ga sakin layi na biyar wanda ke ɗauke da bayani kamar haka; ” duk wanda ke riƙe da ofishin shugaban ƙaramar hukuma, zai bar ofisoshin a ranar da ya cika shekara shida daga ranar farko da ya fara aiki”.

Sai jumla ta uku wacce ke neman kwaskwarima ga sakin layi na 135 a rassa na 2, 2A da na 3 ta hanyar maye gurbin kalmar ‘huɗu’ da ‘shida’ acikinsa.

Sannan, kwaskwarimar ta ƙunshi cewa, idan akwai yaƙi a ƙasa kuma shugaban ƙasa ya ga bai dace a gudanar da zaɓe ba a wannan yanayin, majalisa domin maslaha, tana da damar ƙara masa lokaci kan shekaru shidan. Sai dai tsawon lokacin ba zai wuce wata shida ba.

By Babaji