Rundunar ‘yan sandan Najeriya, reshen babban birnin tarayya, Abuja, a ranar Alhamis, ta dakatar da kwamitin hadin gwiwa, (JAC), na ƙungiyar SSANU da NASU daga gudanar da zanga-zanga a Abuja.
Wakilin jaridar Blueprint ya tattaro cewa jami’an ‘yan sanda dauke da makamai da aka tura da motoci sun tare kofar shiga fitaccen dandalin Unity Fountain da ke Maitama a Abuja.
Kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, CP Benneth Igwe, ya halarci dandalin taron, inda ya shaida wa shugabannin ƙungiyar cewa ba za su yi amfani da titunan Abuja wajen gudanar da zanga-zanga ba ba tare da bayyana dalilin da zai sa su rufe tituna a Abuja.
Sai dai babban sakataren ƙungiyar ta NASU, Peters Adeyemi, wanda ya yi magana a takaice bayan haka, ya shaida wa manema labarai cewa an sanar da hukumomin da suka dace game da shirin gudanar da zanga-zangar.
A cikin Maris din 2022, kungiyoyin sun shiga yajin aikin saboda gazawar gwamnati na mutunta yarjejeniyar da ke tsakanin su.
Sai dai kuma a shekarar 2023, Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin biyan su albashin da aka hana su tare da cire jami’o’i daga tsarin tsarin biyan albashi na IPPIS.
Watanni tara bayan umarnin shugaban ƙasa, kungiyoyin sun zargi gwamnatin tarayya da ƙin mutunta wannan umarnin.
