Daga AISHA ASAS
Mai karatu barkanmu da sake ganin zagayowar sati lafiya. Kamar yadda muka sanar da ku a satin da ya gabata cewa, wannan darasi bai kai ƙarshe ba, don haka da yardar mai dukka, za mu ɗora daga inda muka tsaya.
Idan ba ku manta ba, mun fara koro bayani kan yadda kayan mata da muke tusa wa a farji yake zama barazana ga lafiyar wurin, inda muka tabbatar wa masu karatu cewa, ba dole sai kayan mata da ke da rashin inganci ba, ko suke da rashin tsafta ne kawai za su iya zama barazana ga wurin ba, asalima darasin gabakiɗaya na magana ne kan yadda ingantattun kayan mata ke iya haifar da cutar sanyi.
Idan kun shirya, mu ci gaba da darasin.
Kunga anan ya bambanta da sauran jiki. Shi ya sa aka ce wuri ne da ke buƙatar taka-tsantsan wurin tu’ammali da shi ko yi masa amfani da wasu ababe.
Haka ma idan mun koma ɓangaren kayan ƙarin ni’ima, za a iya samun cikin ababen da aka yi amfani da shi wurin haɗa magungunan akwai wanda zai iya taɓa zaman lafiyar wurin, hakan kuwa zai iya kawar da wani abu da ba a so ya tafi, ko janyo ciwon sanyi.
A baya mun yi bayani kan yadda sanya turare ko sabulai masu ƙamshi kan iya jefa wurin a hatsarin kamuwa da ciwon sanyi, kuma hakan ba yana nufin darasin namu na wannan makon zai kore wannan batu ba, dukkansu za su iya zama silar samuwar ciwon sanyi da ma wasu curuta na daban.
Bincike na masana ya tabbatar kaso mai yawa daga cikin kayan mata da mata ke tusa wa a farjinsu da sunan ƙarin ni’ima na canza tsare-tsaren wurin da tun farko aka halicce mace da su, kuma farjin ke walwala da su.
Abinda nake so mata su gane, farjin mace fa ba mai cin kuɗi wurin kula da shi ba ne, ba kamar fuska ba ce da iya kuɗinki, iya kyan da za ta yi ba, idan za ki riƙe wasu ɗabi’u kawai za ki iya kare wurin, ki samar masa da ƙamshin da ba mai cutarwa ba.
Bari na ba ki misali da ruwan ɗumi, tsare yin tsarki da ruwan ɗumi komai zafi komai sanyi kawai zai iya ba wa mace wani abu da take nema daga wurin. Tsaftace wurin, ta hanyar yawaita canza kamfai, da saurin canja audugar mata a lokacin al’ada, rashin zama a jiƙe, ko zama wuri mai damshi, katange shi daga zuwan ƙwayoyin cuta ta hanyar sa ma sa abinda zai kare shi yayin tafiya ko daga iska da sauransu.
Domin ƙarin bayani ko shawara za ku iya neman wannan lamaba: 08069313321.
