Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Hukumar gudanarwar na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Katsina United ta sallami sakataren ƙungiyar Sale Yusuf daga muƙamin sa.
Babban sakatare a ma’aikatar cigaban matasa da wasanni a Jihar Katsina Muhammad Rabi’u Muhammad ya sanya hannu a takardar da aka rabawa manema labarai.
Ya umarci sakataren da ya miƙa duk wasu kayayyaki mallakar ƙungiyar da ya miƙa su ga hukumar gudanarwa na ƙungiyar.
Babu wani cikakken bayani kan dalilin ɗaukar wannan mataki,sai dai babban sakataren ya yaba wa tsohon sakataren bisa ƙwazo da sadaukar da kai da ya nuna lokacin da ya ke riƙe da muƙamin.
Sai dai magoya bayan ƙungiyar ta Katsina United na kokawa kan yadda ake samun yawaitar canza masu horas da ‘yan wasan ƙungiyar wanda na ɗaya daga cikin abubuwan da ke kawowa ƙungiyar koma baya.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa na Katsina United dai ta ke buga gasar na Firimiya,ta gama wasan a kakan da ta wuce tana na goma sha biyar a teburin gasar.
