Zamfara: Masu zanga-zanga sun caccaki Gwamna Dauda kan ƙamarin rashin tsaro

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu fusatattun mazauna yankin Fagen Mahe, wanda kauye ne da ƴan bindiga suka addaba dake Ƙaramar Hukumar Gusau a Jihar Zamfara, sun gudanar da zanga-zanga biyo bayan wani sabon hari da ya yi sanadin rasa rayukan mutane 20.

A ranar Laraba ne jama’ar, waɗanda galibin su mata ne da matasa, suka yi tattaki daga ƙauyen nasu zuwa Gidan gwamnatin jihar dake Gusau.

An fara zanga-zangar ne cikin lumana kana daga bisani aka fara furucin-baka wajen kokawa game da halin da suka samu kansu a ciki, lamarin da ke ƙara ta’azzara rashin tsaro a yankin nasu.

Sun zargi gwamnan da saɓa alƙawarin da ya yi musu na kawo ƙarshen ta’addanci a mako biyu kacal daga sanda ya fara mulki, inda yanzu ya haura shekaru biyu ba tare da hakan ba, hasali ma ƙara taɓarɓarewa al’amarin ya yi.

Haka kuma, sun soki gwamnan akan nuna gazawarsa wajen gudanar da harkokin gwamnati a yayin tarzoma.

Kazalika, sun bayyana ƙin amince wa kalamansa na kwanan nan da, inda ya ce lamarin rashin tsaro abu ne da ya fi ƙarfin sarrafawa saboda ba shi ke bada umarni ga jami’an tsaro ba.

Zamfara ɗaya ce daga cikin jihohin da ke fama da matsalolin hare-hare daga ƴan bindiga a ƙauyuka da dama dake ƙananan hukumominta.

By Babaji