Gwamnatin tarayya ta yi kunnen uwar shegu da buƙatun talakawa – Abdulmajid Daudu

Spread the love

Daga RABIU SANUSI

An bayyana Gwamnatin tarayya da cewa tayi biris da buƙatun talakawa na dawo da wasu tsaruka da suke sauƙaƙawa al’ummar Najeriya ta fuskoki daban-daban.

Shugaban gamayyar kungiyoyin ‘yan kishin ƙasa wadda akafi sani da(NIGERIA PATRIOTIC FRONT MOVEMENT) na Najeriya Kwamared Abdulmajid Yakubu Daudu ne ya bayyana haka a wani taron manema Labarai da suka kira a ofishinsu.

Kwamared Daudu ya fara bayyana cewa na farko suna buƙatar Gwamnatin Tarayya da ta fara duba batun biyan diyyar waɗanda suka rasa rayukan su a zanga-zangar watan Agusta da ya gabata ga iyalan su.

Kwamared Daudu ya kuma bayyana cewa batun yadda gwamnati ta mayar da harkokin ciwo bashi yayi yawa da ya zuwa yanzu ƙasar na gab da durƙushewa kamar yadda wasu ƙasashe suka samu kansu.

“Yanzu maganar da akeyi akwai natsaloli masu tarin yawa da suke barazana a wanna ƙasar,kama daga hauhawar farashin kayan abinci,tsadar man fetur, da wannan gwamnati ta kasa magance su.”

“Idan kuka kalli maganar cin hanci da rashawa a wannan ƙasa kullum sabon salon yake ɗauka,maimakon a samu sauƙi ƙara gaba yake yi,babu wata hanya da zaka bayyana wannan gwamnati da zaka ce tana taimakon wannan al’ummar ta.

Kwamared Abdulmajid Yakubu Daudu ya ƙara bayyana cewa mafita a wannan ƙasa ya zuwa yanzu shine ta dawo da janye tallafin man fetur da ta janye,sannan ta dawo da batun tsohon tsarin hanyar sadarwa ta NITEL dan sauƙaƙawa al’ummar Najeriya.

Shugaban gamayyar ƙungiyoyin ƴan kishin ƙasar ya kuma bayyana buƙatar dawo ma da manoma gonakin su wanda hakan zai taimaka wajen ƙara samun zaman lafiya.

“Muna Kira da babbar murya ga gwamnati ta mai da hankali wajen dawoma da jama’a yaran su, da tun wancan lokacin zanga-zangar su kayi ɓatan dabo a faɗin ƙasar nan.”

Kwamared Daudu yace har yanzu suna nan da ƙudurin gudanar da wata zanga-zangar dan nusar da gwamnati na rashin cika waɗannan alƙawuran da ta ɗaukar ma talakawan ta, na rashin biyawa ƴan ƙasa buƙatun da suka kamata.

Haka zalika Daudu ya ƙara da cewa sukar Gwamnatin Tarayya da haɗiye sauran ham’iyyun adawa wanda hakan ya saɓawa kundin tsarin mulkin Siyasar Najeriya.

“Ya zaman wajibi a tsaida ciwoma ƴan ƙasa bashi daga ƙasashen duniya dan bashi da wani amfani,kuma babu wata hanya da zamu bayyana shi da yake taimakon talakawa.

Daudu ya kuma buƙaci gwamnati da ta mai da mafi ƙarancin albashin ƙaramin ma’aikaci zuwa naira dubu 250,000 ta yadda zai samu damar samun biyan wasu buƙatun da yanzu suka gagare shi musamman abinci da lafiya.

By ukarofi