Daga USMAN KAROFI a Abuja
Gwamnatin Amurka ta fitar da sabon gargadi ga ‘yan ƙasarta game da tafiya zuwa Najeriya, tana mai shawararsu da su sake tunani kafin su yi tafiya zuwa ƙasar, sakamakon yawaitar hare haren ta’addanci, garkuwa da mutane. A sabon rahoton da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta wallafa a matsayin wani ɓangaren na tantance tafiye-tafiye, an saka Najeriya a matakin “Level 3 – Reconsider Travel,” yayin da aka jera wasu jihohi 18 a cikin “Level 4 – Do Not Travel.”
Jihohin da suka shiga cikin wannan matakin na huɗu da aka ƙarfafa kada a je su sun haɗa da Borno, Yobe, Kogi, da Adamawa saboda ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane. Haka kuma, an haɗa Kano, Kaduna, Katsina, Zamfara, Sokoto, Bauchi da Gombe cikin jerin saboda matsalolin hare-haren ‘yan bindiga da garkuwa da mutane da ake fama da su a yankunan.
A Kudancin Najeriya kuwa, an gargaɗi ‘yan Amurka kada su je jihohin Abia, Anambra, Bayelsa, Delta, Enugu, Imo da yawancin sassan jihar Ribas (ban da birnin Fatakwal) saboda yawaitar laifukan da suka haɗa da tashin hankali da garkuwa da mutane. Har ila yau, rahoton ya bayyana cewa hare-haren da ake fama da su a Najeriya sukan faru ne ba tare da tsammani ba, kuma sukan kasance masu hatsari matuƙa a cikin birane da karkara.
Baya ga matsalolin tsaro, rahoton ya nuna damuwa matuƙa kan halin da cibiyoyin lafiya ke ciki a Najeriya, inda aka bayyana cewa yawancin asibitocin ƙasar na fama da ƙarancin ma’aikata, kayan aiki, da rashin kulawa ga marasa lafiya. Gwamnatin Amurka ta shawarci ‘yan ƙasarta da su zo da magungunan su, su ɗauki rigakafin cututtuka da kuma samun inshorar lafiya mai inganci kafin su shigo Najeriya. Masana tsaro na ganin wannan gargaɗi a matsayin kira ga Najeriya domin gyara matsalolin tsaro da lafiyar jama’a.
