Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shekaru 16 da rasuwar ‘Yar’adua: Ƙungiyar ɗalibai reshen jami’ar UMYUK ta shirya taro kan nagartar shugabancin marigayi tsohon shugaban ƙasa marigayi Umaru Musa Yar’adua da karrama shi da lambar yabo.
Ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa reshen jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina (SUG UMYUK) ta shirya babban taro na musamman domin tunawa da cikar shekaru 16 da rasuwar tsohon shugaban ƙasa, marigayi Malam Umaru Musa ‘Yar’adua, tare da haskaka kyawawan halayensa da kuma irin nagartar shugabancinsa.
Taron mai taken “Nagartar Shugabanci: Gaskiya da hidimar jama’a” ya gudana ne a babban ɗakin taro na jami’ar, inda aka mayar da hankali kan yadda za a gina shugabanci mai inganci da kishin jama’a bisa koyarwar marigayin.
A jawabinsa na maraba, shugaban ƙungiyar daliban jami’ar, Abubakar Ahmed, ya bayyana cewa taron ba kawai taro ba ne, illa wata muhimmiyar dama ta koyon darussa na shugabanci ga ɗalibai, yana nuni da mahimmancin koyi da rayuwar marigayi Yar’adua ga ɗalibai.
“A yau ba kawai mun taru domin tunawa da marigayi ‘Yar’adua ba ne, mun taru ne domin mu yi tunani a kansa, mu fahimci darussan rayuwarsa, sannan mu ɗauki darasi daga gare sa.” In ji shi.
Ya ƙara da cewar “Shugabanci na gaskiya ba a auna shi da iko ba ne, sai da gaskiya; ba da mukami ba ne, sai da hidima; kuma ba da magana ba ne, sai da tsayawa kan ƙa’ida.” In ji Ahmed.
A maƙalar da ya gabatar a taron, babban baƙo a taron tunawa da marigayin, Ministan Gidaje da raya Birane, Injiniya Dakta Muttaqa Rabe Darma, ya bayyana Malam Umaru Musa ‘Yar’adua a matsayin muhimmin misali ga shugabanci na gaskiya a Nijeriya, maƙalar da ya yi wa take da: “Rayuwar Hidima: Falsafa da Aiwatar da Gaskiya a Shugabancin Umaru Musa ‘Yar’adua.”
Ministan ya bayyana kamanta gaskiya a mulki a matsayin ginshiƙin shugabanci nagari, yana mai cewar “Gaskiya ba wata dabara ta siyasa ba ce, illa hanya ce ta rayuwa. Kuma hidimar jama’a, amanar Allah ce da ba za a iya sauke ta yadda ya kamata ba sai da gaskiya.” In ji Darma.
Ya bayyana marigayin a matsayin shugaba mai natsuwa da tsoron Allah, yana mai cewar, “Ya tafiyar da mulki cikin mutunci da nutsuwa,” inda ya ce abin da wasu su kuma ke ɗauka a matsayin rauni, “amma tarihi na kallon ‘Yar’adua a matsayin mai kyakkyawar ɗabi’a,” In ji Darma.
Harwayau, naƙalar tasa ta ƙara bayyana wasu muhimman darussa daga rayuwar marigayin, yana mai zayyana cewar; “Muhimmancin gaskiya a rayuwa da shugabanci, duba shugabanci a matsayin amanar jama’a ba mallaka ba, ƙarfafa ilimi a matsayin ginshiƙin ci gaban ƙasa, bin doka da oda a harkokin mulki, ƙarfafa tsarin riƙon amana da gaskiya a gwamnati” a matsayin misalan siffofin da marigayin ya wanzu da su a rayuwarsa da ya kamata masu shirin shiga fagen shugabanci su yi koyi da su.
Darma wanda ba hannun marigayi Umaru Musa Yar’adua ne tun yana gwamnan jihar Katsina kafin ya zama shugaban ƙasa ya hori ɗaliban da su rungumi darussa daga rayuwar Marigayi Malam Umaru Musa ‘Yar’adua; rayuwa mai cike da hidimtawa al’umma, ba rayuwar son kai ko wawure dukiyar al’umma ba.
“Bayan shekaru 16 da rasuwar Malam Umaru Musa ‘Yar’adua, har yanzu darussan rayuwarsa na da matuƙar muhimmanci ga sabbin shugabanni.
Ƙalubalen da ke gaban Nijeriya a yau ba rashin misali ba ne, sai rashin koyi da misalin da muka riga muka samu,” Darma ya ce.
A wajan taron, an gudanar da zaman tattaunawa tsakanin masana kan batun nagartar shugabanci, inda aka tattauna tare da ƙara fito da wasu darussa daga rayuwar marigayin.
Kungiyar ɗalibai na jami’ar ta kuma karrama marigayi Malam Umaru Musa ‘Yar’adua da lambar yabo ta musamman kan gudummawar da ya bayar wajen kafa shugabanci nagari, inda Ministan ya karɓa a madadinsa.
Taron dai ya samu halartar mutane daga ɓangarori daban-daban, ciki har da dansiyasa, Hon. Salisu Yusuf Funtua, Shugaban majalisar matasa ta ƙasa, Yusuf Abubakar Papa; Malamai daga jami’o’in UMYUK da FUDMA; Ɗalibai da sauran masu ruwa da tsaki a fannin ilimi da sauran masu fafutikar kafuwar shugabanci nagari.
