Shin ko kin san man jojoba?

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Kwalliya na jaridar al’umma, Blueprint Manhaja. Muna jinjina maku kan yadda ku ke bibiyar mu a kodayaushe. 

A wannan makon shafin ya ɗan yi nisan kiwo, inda ya zaƙulo maku ɗaya daga cikin ababe masu matuƙar tasiri ga lafiyar fata, saidai sun ɗan nisanta daga idanuwanmu, dalilin rashin wanzuwar sa sosai a ƙasar Hausa. 

Da wannan ne za mu soma da shimfiɗa kan shi karan kansa man na jojoba kamar yadda ake kiransa, kafin mu tsunduma cikin darasin namu.

Shin mene ne ake kira da man jojoba?

Jojoba oil kamar yadda ake kiransa, wani sinadari ne mai ban sha’awa da ake samu daga tsirrai, wanda a zahiri ba mai ba ne kai tsaye, illa wani irin nau’in ruwa masu kama da madara, masu haske “liƙuid waɗ” da ke kama da kitse na halitta da fata ke samarwa (sebum). Wannan sifar tasa ta musamman ce ke sa ya dace da kusan kowane irin fata, daga mai masƙi, zuwa busasshiya, har ma da fata mai saurin kamuwa da kuraje.

Masana kula da fata sun tabbatar da cewa wannan man yana da ikon shiga cikin fata cikin sauƙi ba tare da toshe ramukan fata ba, lamarin da ke sa ya zama mafita ga masu fama da matsalolin fata daban-daban.

By ukarofi