
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Al’umma a Gundumar Nahuce da ke Ƙaramar Hukumar Bunguɗu ta Jihar Zamfara sun koka game da ta’azzara da rashin tsaro a yankunansu.
Daga cikin ƙauyukan da al’amarin ya shafa akwai Zagi, Ɗanguro, Leƙa, Mallamawa da sauransu, waɗanda a yanzu suke fuskantar mawuyacin hali game da tsaron rayuka da dukiyoyinsu daga farmakin ‘yan bindiga.
A wani saƙon murya da Shugaban ƙungiyar ‘yan gwan-gwan ta ƙasa, Muntari Muhammed ya fitar wa Manhaja, ya ce jama’ar yankunan suna fuskantar matsi na kashe-kashe, sace-sace da kuma ɗaiɗaita gidajensu daga ‘yan bindiga a yankin.
A cewarsa, akwai wata daba ta ‘yan bindiga a yammacin waɗannan ƙauyuka da ake zargi da ƙone gidaje, garkuwa da mutane da kuma halaka wasu da dama a yankin.
Ya bayyana cewa, a kan samu yankin da babu koda ɗan bijilante da ke zuwa sintiri balle jami’an tsaro, lamarin da ya ba ‘yan ta’addar damar cin karensu ba babbaka tare da tilasta wa wasu da dama barin muhallansu domin neman mafaka a wasu wurare.
Akan haka ne ya yi kira ga hukumomin tsaro da su kawo wa yankunan ɗauki domin ceto al’umma daga halin da suka samu kansu a ciki.
Ya ƙara da cewa, akwai dabar da wani sanannen ɗan bindiga mai suna Ɗan Sadiya ke jagoranta, wadda ya alaƙanta da hannu a addabar yankunan nasu.
A ƙarshe, ya yaba wa jami’an hukumomin tsaro bisa jajircewa wajen ƙoƙarin daƙile ayyukan ta’addanci a sassan jihar, yana mai kira a gare su da su kai wa yankin nasu agaji.

