A ƙarshe, Ganduje ya kira da Sanusi a matsayin Sarkin Kano

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Talata tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana amincewa da Alhaji Muhammadu Sanusi na II a matsayin Sarkin Kano kuma Shugaban majalisar sarakunan Kano.

Ganduje ya bayyana haka ne yayin taron rantsar da sabon mataimakin gwamnan jihar Kano, Murtala Sule Garo a Gidan Gwamnatin jihar..

A yayin jawabinsa, tsohon gwamnan ya yi gaisuwa ga Sanusi da kiran sa da cikakken sunan sarauta, lamarin da mahalarta taron suka yaba wa.

Wannan shi ne karo na farko da Ganduje ya bayyana a fili ɗaukar Sanusi a matsayin sahihin wanda ke riƙe da kujerar sarautar.

By Babaji