
Daga BELLO A BABAJI
Ƙungiyar Amnesty International ta yi alla-wadai da Shugaba Bola Tinubu kan kai samame da jami’an DSS suka yi a ofishin cibiyar tabbatar da Ƴanci da Adalci, SERAP.
A ranar Litinin ne SERAP ta sanar da al’umma ta kafarta ta X cewa, jami’an DSS sun y wa ofishinta da ke Abuja ƙawanya.
SERAP ta yi kira ga Shugaba Tinubu ya gaggauta umartar DSS ta daina kai hari da cin mutuncin ƴancin ƴan Nijeriya.
A lokacin da ta ke magana game da batun, Amnesty International ta nuna damuwa kan matakan da gwamnatin ke ɗauka inda ta ce Tinubu na ɗaukar salon matsi da tauye haƙƙin Ɗan-adam a gwamnatinsa.
Ta ce, sun samu saƙon kai samame ba bisa ƙa’ida ba da jami’an DSS suka yi a ofishin SERAP wanda hakan ya haifar da cecekuce a cikin al’umma tare da samun kiraye-kiraye na a dakatar da ire-iren haka ga ƙungiyoyi masu zaman kansu da cibiyoyin kare ƴancin Ɗan-adam a Nijeriya.
