Dalilan zuwanmu ofishin SERAP – DSS

Spread the love

Hukumar ƴan sandan farin kaya DSS sun bayyana dalilan su na zuwa ofishin ƙungiyar SERAP a Abuja.

Hukumar ta musanta zargin da ke yawo ta kafafen sadarwa cewa, sun ci zarafin ma’aikatan ƙungiyar wanda a gaskiya ba haka bane. Hukumar ta bayyana cewa ziyarar da su ka kai ziyarace da an saba kai irin ta ba wai ta tuhuma ba ce.

Don haka hukumar ta yi kira da ƴan Nijeriya su yi watsi da duk wata jita-jita da ake yaɗawa da sunan sun ci zarafin ƙungiyar domin a gaskiya ba haka abun yake ba. Hasali ma, ma’aikatan hukumar da suka ziyarci hukumar ba sa ɗauke da wasu makamai kuma su biyu ne kacal.

Sai dai ƙungiyar SERAP a bayanin da fitar ta nuna ba haka abun ya ke ba domin har sun yi kira da shugaba Tinubu ya umarci hukumar su daina wannan cin zarafin ƙungiyar da kuma sauran ƙungiyoyin masu zaman kansu da a ke cin zarafin su.

By ukarofi