Ambaliyar ruwa ya mamaye sassa daban-daban a birnin Maiduguri

Spread the love

Daga USMAN KAROFI a Abuja

Dubban jama’a sun fice daga gidajensu sakamakon wata mummunar ambaliyar ruwa da ta afku a wasu sassan Maiduguri babban birnin Jihar Borno.

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa galibin wuraren da lamarin ya shafa suna cikin ƙaramar hukumar Jere.

A baya dai gwamnatin Jihar Borno ta bayar da umarnin rufe makarantu saboda rahotannin da ke cewa ambaliyar ruwan na iya ta’azzara cikin sa’o’i 48 a jihar.

Wakilinmu ya tattaro cewa lamarin wanda ya faro tun mako guda da ya gabata ya kai ƙololuwa a safiyar yau Talata.

Yawancin mazauna unguwannin Fori, Galtimari, Gwange, da Bulabulin sun yi hijira.

Gidan Watsa Labarai na Jiha BRTV da Post Office, Shehu Laminu way, da Custom Area, suma ambaliyar ruwan ya riske su.

Wata majiya ta shaida wa Manhaja cewa Dam ɗin Alao ya ruguje da sanyin safiyar Talata, inda ya yi matuƙar barazana ga mazauna Maiduguri.

A cewar wani da lamarin ya shafa, ruwan ya mamaye gadar Fori, wacce ta haɗa Fori da Galtimari zuwa Tashan Bama, ta kuma ratsa gidaje da ƙarfin gaske.

“Kowa ya guje wa gidan waya, Monday Market har ma da hanyar da ke bayan gidan zoo tare da tashar mai ta Hissan saboda ambaliya ta mamaye dukkan wannan hanyar” inji wani mazauni

Wani mazaunin Galtimari ya ce: “An sanar da mu cewa mu kwashe kayanmu da ƙarfe 12:30 na safe, amma kafin mu tattara kayanmu da takardun shaidar makaranta, ruwan ya riga ya cika a gidanmu.

Wani ɗan jarida da ke aiki da gidan talabijin na Borno (BRTV) ya ce ” Yankin Post Office da ofishinmu na BRTV duk mamaye su ke da ruwa”.

Wani mazaunin garin, Bilyaminu Yusuf ya ce, “Muna cikin wani mawuyacin hali a kan titin Legas da ruwa ya mamaye, sai da muka gudu zuwa makarantar firamare ta Galtimari, inda muka bar yawancin kayayyakinmu.”

Wakilinmu da ya ziyarci wasu yankunan da lamarin ya shafa, ya tabbatar da cewa ruwan ya mamaye gadar Legas, ɗaya daga cikin gada mafi girma a cikin birnin.

An tilasta wa mazauna da yawa barin gidajensu tare da neman mafaka a wani wuri, yayin da wasu ke ɗauke da kayansu suna neman mafaka.

By ukarofi