Ƙungiyar APUA ta yi fatali da tsarin karɓa-karɓar shugabanci a Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ƙungiyar Haɗin Kan Al’ummar Arewacin Nijeriya (APUA) mai zaman kanta kuma mai rijista, ta yi fatali da yarjejeniyar tabbatar da tsarin karɓa-karɓan shugabanci a Nijeriya tsakanin Arewa da Kudu, inda ta bayyana hakan a matsayin saɓa ƙa’ida, rashin bin tsarin dimokuraɗiyya da kuma rashin bin tsarin mulkin ƙasa.

A cikin wata sanarwar manema labarai da shugaban ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Adamu Aliyu ya sanya wa hannu, APUA ta yi nuni da cewa yarjejeniyar ba ta cikin Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya, don haka ba ta da wani tasiri a kan masu zaɓe.

Matsayin ƙungiyar ya biyo bayan kalaman da wasu fitattun ‘yan siyasa a baya-bayan nan da suka haɗa da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nelson Wike, da tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ke nuna cewa mulki ba zai dawo Arewa ba har sai 2031 tare da yin nadamar tsayawa takarar mataimakin shugaban ƙasa tare da Atiku Abubakar a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

ƙungiyar ta APUA ta kuma yi tsokaci kan wata sanarwa da ƙungiyar Oodua Peoples Congress ta fitar, inda ta zargi wasu jiga-jigan siyasar Arewa da ƙoƙarin tsige shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kafin ƙarewar wa’adin mulkin sa.

“Muna tambayar su wane ne a Arewa da Kudu suka yi wannan yarjejeniya kuma da yardar wa?” 

ƙungiyar ta jaddada cewa dimokuraɗiyya wasa ce ta lambobi kuma ba ta da gurbin bin tsarin karɓa-karɓan shugabanci ko yanki, abin da ta bayyana a matsayin ƙirƙiro jam’iyyun da ba su da goyon bayan tsarin mulki.

ƙungiyar ta APUA ta kuma bayyana damuwarta kan wasu batutuwan da suka kunno kai gabanin babban zaɓen ƙasar na 2027, da suka haɗa da yunƙurin soke wasu tanade-tanade na dokokin zaɓe da suka shafi tantance masu kaɗa ƙuri’a da kuma yiwuwar gudanar da ƙidayar jama’a ta fuskar tsaro.

ƙungiyar ta sanar da shirin fara wayar da kan ’yan Arewa kan zaɓen shugaban ƙasar Nijeriya kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin ƙasar ya tanada, a kan yaƙi da tsarin karɓa-karɓan shugabanci ko yankin da bai zama tilas ba.

By ukarofi