Ƙungiyar Izala ta raba wa marayu kayan sallah a Kano

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Ƙungiyar Izala, reshen jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Farfesa Abdallah Saleh Pakistan, Shugaban Hukumar Aikin Hajji ta ƙasa ta raba kayan abinci da sutura  ga marayu.

An ƙaddamar da rabon tallafin ne a harabar masallacin Juma’a na Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam da ke unguwar Tudun Murtala.

Da yake jawabi a madadin shugaban ƙungiyar Izala na Jihar Kano Farfesa Abdalla Saleh Pakistan wanda ya sami wakilcin mataimakin shugaban ƙungiyar na ɗaya.

Malam Muhammad Ahmad Usman Bichi yace a baya shugaban ƙungiyar ne ke jagorantar rabon tallafin, amma wannan karon saboda hidimar ƙasa da aka ɗora masa na aikin hajji bai sami dama ba, don haka yake ƙaddamar da rabon a madadinsa.

Ya ce, ana raba kaya da yawa a baya  amma kowane yanayi da yanda yake zuwa, saboda haka abin ya sawwaƙa shi aka bayar.

Ya ja hankalin al’umma  talakawa da masu hali akan su riƙa ƙoƙarin tallafawa marayu da abinda suke dashi domin kullum marayu ƙara yawa suke  zaka tarar akwai mutane da ake tare dasu bara bana babu su sun tafi sun bar marayu.

Malam Ahmad Muhammad Usman Bichi ya yi kira ga masu kula da marayu su daure suyi haƙuri su basu tarbiyya ta gari da kyakkyawan kulawa yanda zasu taso su zama masu amfani a cikin al’umma.

A nasa jawabin sakataren kwamitin rabon tallafin  marayun. Malam Sani Jibrin ya ce a bana ma sun tattara, tallafi da suke samu na kwamitin masallaci dana ɗaiɗaikun mutane da kuma wanda suke samu daga wasu fitattun mutane.

Ya ce, daga gudummawa da suka samu akwai kudi N5,000,000 daga Alhaji Aminu ɗantata da N1,000,000 daga Alhaji Ibrahim ɗanyaro. Alhaji Haruna Tahir Hungu N1,000,000 Shugaban hukumar aikin hajji na ƙasa. Farfesa Abdallah Saleh Pakistan ya bada N200,000.

Ya ƙara da cewa akwai mutane da dama da suka bada gudunmuwa.Haka Alhaji Auwal Abdullahi Rano bana ya bayar da buhunan shinkafa 150. Tsohon mataimakin Gwamnan Kano Dakta Nasir Yusuf Gawuna  na daga waɗanda suka bada gudunmuwa.

Malam Sani Jibrin ya ce a bana an sami tara kaya da kuɗi na sama da N16,000,000 kuma marayu sama da 3000 ne suka amfana daga ƙananan hukumomi 44 na jahar Kano a tsarin bana, wasu an basu kayan abinci da kuɗin cefane wasu kuma an basu sutura sannan akwai shiri na horar da marayu akan sana’o’i na dogaro da kai.

By ukarofi