JEDDA na neman gudunmawar Gwamnan Kano – Maishinku

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

Kungiyar Masu Kasuwancin Sayar da Sarƙoƙin da ɗan Kunne, wadda ake kira da ƙungiyar JEDDA ta masu sana’ar yari ƙarƙashin shugabanci Alhaji Yakubu Maishinku, na neman gudunmawa Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf a kan duk wani abu da ke tallafawa ƙungiyoyi domin cigaban su.

Ya bayyana cewa, wannan ƙungiya na neman gudunmawar da za su bunƙasa harkar kasuwancin su ta yau da kullum wacce dubban matasa ke ƙarƙashinta domin cigaba da bunƙasa kasuwancinsu wanda amfani ne na kano da al’ummar ta dama Nijeriya baki ɗaya.

Har ila yau, Maishinku ya bayyana cewa bisa la’akari da yadda hidimar azumi da kuma hada hadar sallah ƙarama da ake ciki tuni wannan ƙungiya ta umarci ɗaukacin ’ya’yanta da su zaftare farashin kayayya kin su domin sauƙaƙawa al’umma a wannan lokaci da buƙatar kayayyaki su ka ƙaru wajan al’umma wanda kuma ya bayyana cewa wannan umarni na ƙungiyar JEDDA ya samu karɓuwa daga ’ya’yanta idan kuma ya yabamusu kan irin haɗin kan da ƙungiyar take samu daga ’ya’yanta ’yan kasuwa da ake tare da kuma MD na kasuwarsabon garida sauran masu ruwa da tsaki a harkar kasuwanci a kano da ƙasa baki ɗaya.

Tun da farko sai da ya yabawa gwamnan kano Alhaji Abba Kabiru Yusuf kan yadda yake aikin ciyarda kano ta kowana fanni kamar ilimi, Lafiya, Tsaro, inganta birnin kano da sauran ƙananan hukumomi inda kuma ya yabawa gwamnan kan naɗa musu Alhaji Abdul Bashir Usaini, a matsayin shugaban kasuwa sabon gari da kuma yadda yake gudanar da aikinsa a wannan kasuwa inda a ƙarshe ya yi addu’ar zaman lafiya da ƙaruwar arziƙi a kano Nijeriya da ma duniya baki ɗaya.

By ukarofi