Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arzikin ƙasa Ta’annati (EFCC) ta gurfanar da wasu mutane huɗu a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Ikoyi, Jihar Legas, inda aka yanke musu hukuncin ɗaurin watanni biyu zuwa shida bisa laifin gudanar da harkokin musayar kuɗin waje ba ta hanyar da doka ta tanada ba, da kuma safarar takardun kuɗin naira ba bisa ƙa’ida ba.
Waɗanda kotun ta samu da laifi su ne Ahmad Umar Baros, Aminu Umar Injay, Yusuf Suleimon da Olasunbo Sholanke. Hukuncin ya fito ne daga Mai Shari’a F.N. Ogazi, bayan Daraktar Yankin Legas na 1 ta EFCC ta gurfanar da kowannensu kan tuhumar daban-daban.
An zargi Baros da gudanar da hada-hadar musayar kuɗin waje a shekarar 2026 a Jihar Legas, ba tare da amfani da kasuwar musayar kuɗin waje da gwamnati ta amince da ita ba, abin da hukumar ta ce ya saɓa wa tanadin Dokar Kafa Kwamitin Leken Asiri kan Tattalin Arzikin ƙasa ta 1994.
Shi kuwa Yusuf Suleimon da Olasunbo Sholanke, an tuhume su ne da sayarwa da safarar takardun naira da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya fitar. Dukkan waɗanda ake tuhumar sun amsa laifinsu bayan an karanta musu tuhumar da ake yi musu a gaban kotu.
Bayan amincewarsu da aikata laifin, lauyoyin masu gabatar da ƙara, N.K. Ukoha, Ebuka Okongwu da U.S. Kyari, sun gabatar da bayanan shari’o’in tare da roƙon kotu ta yanke musu hukunci bisa laifukan da suka amsa.
A hukuncinsa, Mai Shari’a Ogazi ya tabbatar da samun dukkan huɗun da laifi. Kotun ta yanke wa Ahmad Umar Baros hukuncin ɗaurin watanni biyu a gidan yari, yayin da Aminu Umar Injay, Yusuf Suleimon da Olasunbo Sholanke suka samu hukuncin watanni shida kowannensu, tare da zaɓin biyan tarar Naira 100,000 maimakon zaman gidan yari.
