Hukumar NERC ta tsige daraktocin Kamfanin Rarraba Wutar Lantaki na Kaduna kan bashin Naira biliyan 456.5

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Kula da Harkokin Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC) ta rushe kwamitin gudanarwar Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kaduna (KAEDC), sakamakon tarin bashin da kamfanin ya kasa biyan kasuwar wutar lantarki wanda ya kai kusan Naira biliyan 456.5.

Hukumar ta kuma naɗa wani kwamitin riƙon ƙwarya na musamman, tare da umartar a fara wani tsari na gaskiya da gasa domin nemo sabon babban mai zuba jari da zai karɓi ragamar kamfanin.

Matakin na NERC yana ƙunshe ne cikin Umarni mai lamba NERC/2026/086, mai taken “Umarni kan shiga tsakani a harkokin Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kaduna bisa Dokar Wutar Lantarki ta 2023”, wanda ya fara aiki ranar Litinin, 10 ga Agusta, 2026.

NERC ta ce ta ɗauki matakin ne bayan gudanar da bincike da tuntubar manyan masu ruwa da tsaki a harkar wutar lantarki, ciki har da Hukumar Kula da Kamfanonin Gwamnati (BPE).

Hukumar ta ce KAEDC ya daɗe yana kasa cika wasu wajibai na doka da na kasuwar wutar lantarki, yayin da rashin isasshen jari da raunin gudanarwa da harkokin kasuwanci suka kara taɓarɓarewar kamfanin.

A cewar NERC, zuwa watan Mayun 2026, bashin KAEDC na wajibcin kasuwar wutar lantarki tun bayan sayar da kamfanin ya kai kusan Naira biliyan 456.5.

NERC ta ce, tun bayan da ASI Engineering Limited ta karɓi ragamar gudanar da KAEDC a watan Yunin 2024, kamfanin ya kara tara bashin kasuwar wutar lantarki da ya haura Naira biliyan 118.6 zuwa watan Mayun 2026. Hukumar ta bayyana cewa a shekarar 2025, KAEDC ya biya kashi 41.93 cikin 100 kacal na kuɗaɗen da aka tsara ya biya a kasuwar wutar lantarki.

Hakan ya haifar da gibin biyan kuɗi da ya kai kusan Naira biliyan 46.71 a cikin shekarar. NERC ta danganta wannan gazawar da yawan asarar wutar lantarki da kamfanin ke fuskanta a ɓangarorin fasaha, kasuwanci da karbar kuɗaɗen wuta. Ta ce jimillar asarar ta kai kashi 71.88 cikin 100 a shekarar 2025.

Wannan na nufin KAEDC ya iya lissafa ko karɓar kuɗin kashi 28.2 cikin 100 kacal na wutar da aka ba shi domin ya rarraba wa masu amfani. Hukumar ta kuma ce ASI Engineering Limited ta kasa cika alƙawarin zuba jarin da ya kamata domin farfaɗo da kamfanin.

A shekarar 2025, ainihin kuɗin da KAEDC ya kashe wajen manyan ayyukan zuba jari ya kai kusan Naira biliyan 2.48, alhali mafi ƙarancin adadin da aka tsara ya kamata ya kashe shi ne Naira biliyan 24.51. Wannan na nufin kamfanin ya samu kashi 10 cikin 100 kacal na abin da aka tanada masa.

Haka kuma, NERC ta ce yawan masu amfani da wutar lantarki da ke da mita a yankin KAEDC ya tsaya tsakanin kashi 33.26 zuwa 35.54 tun bayan da ASI ta karɓi ragamar kamfanin, duk da matakan da aka dauka domin tallafa wa kamfanonin rarraba wutar lantarki wajen samar da mita.

NERC ta ce matsalolin kuɗi na KAEDC sun ci gaba duk da cewa an ba kamfanin sassauci da rangwamen wasu ka’idojin biyan kuɗi da suka kai kusan Naira biliyan 6.58 tsakanin Janairun 2024 da Mayun 2026.

Haka kuma, kamfanin ya amfana da tallafin gwamnatin tarayya da ya kai kusan Naira biliyan 53.79 tun daga Yulin 2018. Hukumar ta ce, ci gaba da gazawar kamfanin na iya jefa masu amfani da wutar lantarki, masu bin kamfanin kuɗi da kuma tsarin kasuwar wutar lantarki baki ɗaya cikin haɗari. Ta kuma gargaɗi cewa matsalar kuɗin kamfanin ta kai matakin da ci gaba da kasancewarsa a kasuwar wutar lantarki zai iya zama barazana ga zaman lafiyar tsarin wutar lantarkin Nijeriya.

By ukarofi

Leave a Reply