Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Malamin addinin Musulunci da ke zaune a Kaduna, Sheikh Dr Ahmad Gumi, ya yi kira da a nesantar da addini daga siyasar jam’iyyu, yana mai cewa bai kamata a jawo batun addini cikin fafatawar siyasa a Nijeriya ba.
Gumi ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook da aka tabbatar a ranar Litinin, yayin da yake mayar da martani kan kalaman da ake dangantawa da Sheikh Sani Yahaya Jingir, Shugaban ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS).
Jingir ya yi waɗannan kalamai ne a wani taron bikin auren gata da aka gudanar a Kano ranar Asabar, inda rahotanni suka ce ya kare tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC na Musulmi da Musulmi, tare da yin kira ga Musulmi su zaɓi Shugaba Bola Ahmed Tinubu saboda ya zaɓi mataimaki ɗan addinin Musulunci.
Kalaman sun jawo suka daga wasu shugabannin Kiristoci, ƙungiyoyin fararen hula da masu fafutuka, waɗanda suka bayyana su a matsayin kalaman da za su iya raba kan al’umma.
Gumi ya ce, ya kamata a yi wa Jingir uzuri kan matsayinsa game da siyasa, yana mai cewa malamin yana gudanar da rayuwarsa a wani yanayi da Musulunci ke fuskantar abin da ya kira tsananin nuna ƙiyayya.
Ya ce, “Ya kamata a yi wa Sheikh Jingir uzuri kan tsauraran ra’ayinsa a siyasa; yana rayuwa ne a tsakiyar wani yanayi mai cike da tsananin nuna ƙiyayya ga Musulunci.”
Gumi ya kuma yi tsokaci kan wata taƙaddama da ta shafi wani mataimakin shugaban jami’a Musulmi a Jihar Filato, yana cewa lamarin ya haifar da cece-kuce duk da cewa mutum Musulmi ne kawai.
Sai dai Gumi ya jaddada cewa yin amfani da addini domin cimma muradun siyasa ba ya taƙaita ga wani ɓangare na siyasa kaɗai.
“Shi ma ’yan adawa ba su tsira daga amfani da addini wajen neman ƙuri’u ba,” inji shi.
Ya buƙaci ’yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki su guji mayar da addini makamin fafatawar siyasar jam’iyyu, yana mai cewa ya kamata a mutunta bambancin addinai da ke tsakanin al’ummar Nijeriya.
“Ina ganin a ƙasa mai bin addinai daban-daban, bai kamata a jawo addini cikin ramin ƙazantar siyasa ba,” inji Gumi.
A wani ci gaba, reshen Jama’atu Nasril Islam (JNI) na Jihar Filato ya nesanta kansa da kalaman da ake danganta wa Sheikh Jingir dangane da tikitin takarar shugaban ƙasa na Musulmi da Musulmi.
Wannan matsaya ta biyo bayan wani rahoto da aka danganta wa mataimakin hulɗa da kafafen yaɗa labarai na ƙungiyar, Abdulsalam Ahamed, wanda ya yi iƙirarin cewa JNI ta Filato ta goyi bayan matsayar Jingir.
Sai dai Sakataren Yaɗa Labarai na JNI a Filato Gambo Hamza, ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya da yaudara. Ya ce, “Reshen JNI na Jihar Filato yana bayyana a sarari cewa wannan wallafa da kuma kalaman da aka danganta wa ƙungiyar ƙarya ne, ba su da tushe kuma ba sa wakiltar matsayin JNI na Filato.”
Hamza ya ce Jingir yana da ’yancin bayyana ra’ayinsa na ƙashin kansa, amma bai kamata a gabatar da irin wannan ra’ayi a matsayin matsayin hukuma na JNI ba.
Ya ce, ƙungiyar tana aiki ne domin inganta zaman lafiya, haɗin kai, fahimtar juna tsakanin mabiya addinai da kuma zaman tare cikin lumana tsakanin al’ummomin Nijeriya masu bambancin addini. Ya jaddada cewa JNI Filato ba ta amince da wani bayani da ke nuna cewa ta goyi bayan Sheikh Jingir kashi 100 bisa 100 kan batun tikitin Musulmi da Musulmi ko kuma wani matsayi na siyasar jam’iyya ba.
ƙungiyar ta kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da bincike kan zargin yin amfani da sunanta ba bisa ƙa’ida ba, tare da hukunta waɗanda aka samu da hannu a lamarin bisa tanadin doka.
Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, shi ma ya nuna damuwa kan kalaman Jingir. Kwankwaso ya bayyana matsayinsa ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook da aka tabbatar a ranar Litinin, inda ya ce ya kamata a yi watsi da duk wani furuci da zai iya haifar da rarrabuwar kawuna, musamman idan fitattun shugabannin addini ne suka furta shi.
Ya ce, “Ya kamata a bayyana a fili cewa mutanen kirki na Kano ba sa amincewa ko goyon bayan waɗannan kalamai masu rarrabuwar kai.”
Ya buƙaci shugabannin siyasa da na addini su kasance masu riƙe da gaskiya, su ƙarfafa haɗin kan al’umma, tare da samar da hanyar sulhu da fahimtar juna a ƙasar.
