Yadda na samu rancen biliyan N2.5 domin zuba jari a harkar noma — Buni

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayyana yadda ya samu rancen Naira biliyan 2.5 daga Bankin Noma na ƙasa (BoA) da Bankin Masana’antu (BoI) jim kaɗan bayan hawansa mulki a shekarar 2019, domin zuba jari a harkar noma da bunƙasa tattalin arzikin jihar.

Buni ya ce ya samu Naira biliyan biyu daga Bankin Masana’antu, yayin da ya samu ƙarin Naira miliyan 500 ta wani shirin shiga tsakani na Babban Bankin Nijeriya (CBN), wanda Bankin Noma ya jagoranta.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a Gidan Gwamnatin Jihar Yobe da ke Damaturu.

Ya kuma yi kira ga ma’aikatan gwamnati da su kasance masu gaskiya, riƙon amana da sadaukar da kai wajen gudanar da ayyukansu, yana mai cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci sakaci a wajen aiki ba.

Buni ya ƙarfafa wa ma’aikatan gwamnati gwiwa su rungumi noma da kiwon dabbobi, yana mai cewa dokokin aikin gwamnati ba su hana ma’aikata gudanar da irin waɗannan ayyuka tare da aikinsu na gwamnati ba.

A cewarsa, noma da kiwon dabbobi na daga cikin hanyoyin da za su taimaka wa ma’aikata wajen samun ƙarin kuɗin shiga tare da shirya kansu domin rayuwa bayan ritaya.

“Lokacin da na zama gwamna a shekarar 2019, ɗaya daga cikin abubuwan farko da na yi shi ne samun rancen Naira miliyan 500 daga Bankin Noma ƙarƙashin wani shiri na Babban Bankin ƙasar nan.

“Bankin Masana’antu kuma ya ba ni Naira biliyan biyu, waɗanda na zuba a sayen filayen noma da gudanar da ayyukan noma,” in ji Buni.

Ya ce gonakin da aka kafa sun samar da ayyukan yi ga mutane da dama, waɗanda ke samun abin dogaro da iyalansu ta hanyar ayyukan da ake gudanarwa a gonakin.

“Idan kuna son tabbatar da hakan, ku fita daga cikin gari ku ga gonakin mutanen da ke aiki a can kuma suke samun abin rayuwa daga gonakin. Wannan abu ne da ke ba ni gamsuwa sosai,” in ji shi.

Gwamnan ya bayyana noma a matsayin wani muhimmin jari da zai taimaka wajen rage ƙalubalen da ma’aikata za su iya fuskanta bayan ritaya, tare da samar musu da hanyar samun abin dogaro na dogon lokaci.

“Mafita daga tsoron barin aikin gwamnati ita ce rungumar noma da kiwon dabbobi, domin hakan zai taimaka muku sosai bayan kun yi ritaya,” inji shi.

Buni ya kuma yi kira ga matasa da manoma a jihar da su yi amfani da damar noman rani, yana mai cewa shirin gwamnati na raba famfunan ban ruwa zai taimaka wajen sauƙaƙa harkar noma da ƙara yawan amfanin gona.

By ukarofi