Nijeriya ta kashe tiriliyan N3.14 wajen biyan bashin cikin gida a zangon farko na 2026 – DMO

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ofishin Kula da Basussukan ƙasa (DMO) ta ce Gwamnatin Tarayya ta kashe Naira tiriliyan 3.14 wajen biyan bashin da ta biyo na cikin gida a zangon farko na shekarar 2026.

Jaridar Tribune ta rawaito cewa wannan na ƙunshe a cikin rahoton da DMO ta fitar kan basukan da ake bin gwamnatin Nijeriya a cikin gida, inda ya baiyana cewa cikin kudin, an kashe Naira tiriliyan 2.97 wajen biyan kudin ruwa na bashin, yayin da aka biya Naira biliyan 169.68 a matsayin wani bangare na gundarin bashin.

A watan Janairu, gwamnati ta kashe Naira biliyan 741.82 wajen biyan bashin cikin gida, sannan kudin ya karu zuwa Naira biliyan 967.67 a watan Fabrairu.

A watan Maris kuma, kudin ya tashi zuwa Naira tiriliyan 1.43, wanda ya sa jimillar kudin da aka kashe cikin watanni ukun farko na shekarar ta kai Naira tiriliyan 3.14.

DMO ta ce kudin ruwa ya dauki kaso mafi yawa na abin da gwamnati ta kashe wajen biyan bashin cikin gida, inda ya kai kusan kashi 94.6 cikin 100 na jimillar kudin.

Rahoton ya nuna cewa bashin gwamnati ya karu zuwa Naira tiriliyan 159.35 a zangon farko na shekarar 2026.

By ukarofi