Daga RABIU SANUSI a Kano
Jihar Kano ta zama cibiyar wani muhimmin bincike da Cibiyar Nazarin Manufofi da Dabarun ƙasa ta Nijeriya (NIPSS) ke gudanarwa, domin tantance irin gudunmawar da jihar ke bayarwa wajen bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya, samar da ayyukan yi da haɓaka harkokin kasuwanci.
Tawagar NIPSS, wadda ta ƙunshi mahalarta Babban Darasin Gudanarwa na 48, Rukuni na ɗaya, ta fara ziyarar nazari ta tsawon mako guda a Kano, inda za ta tattauna da gwamnati, ’yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki.
Shugaban tawagar, mai ritaya Birgediya Janar Jimo, MNI, ya bayyana cewa binciken ya mayar da hankali ne kan “Harkokin Tattalin Arziƙi da Kasuwanci na Yanzu domin Samun Ci gaba Mai ɗorewa a Nijeriya.”
A lokacin ziyarar da tawagar ta kai Gidan Gwamnatin Kano, Shugaban Ma’aikatan Gwamna Abba Kabir Yusuf, Dakta Sulaiman Wali, MNI, wanda ya wakilci gwamnan, ya gabatar mata da bayani kan manufofi, shirye-shirye da nasarorin gwamnatin jihar, musamman a fannonin tattalin arziƙi da bunƙasa harkokin kasuwanci.
Haka kuma, Babban Sakataren Ma’aikatar Kimiyya da ƙirƙire-ƙirƙire, Alhaji Abba Danguguwa, ya gabatar da bayani kan shirye-shiryen gwamnati na haɓaka ƙirƙire-ƙirƙire, fasaha, tattalin arziƙi da kasuwanci.
Tawagar ta kuma kalli wani faifan bidiyo da ya bayyana ayyuka da nasarorin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda Daraktan-Janar mai kula da Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, ya shirya, yayin da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan, Mustafa Muhammad, ya gabatar da shi.
Shugaban tawagar ya ce NIPSS ta gudanar da bincike na farko kafin zuwanta Kano, amma ziyarar ta zama wata dama ta tabbatar da bayanan da aka samu tare da jin ra’ayoyin jami’an gwamnati, ’yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki kai tsaye.
Ya ce an zaɓi Kano ne saboda muhimmiyar rawar da jihar ke takawa a tattalin arzikin Nijeriya, musamman ta fuskar albarkatun ɗan Adam, kasuwanci, kamfanoni masu zaman kansu, fasaha, al’adu, yawon buɗe ido da sauran harkokin tattalin arziƙi.
Ya ƙara da cewa bayanan da za a tattara za su kasance wani muhimmin ɓangare na rahoton ƙasa da za a gabatar wa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a ƙarshen darasin.
Ya jaddada cewa tawagar ba ta zo Kano ne domin gudanar da binciken laifi ba, sai dai domin nazarin hanyoyin da gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki za su bi wajen ƙarfafa tattalin arziƙin ƙasa, samar da ayyukan yi ga matasa da bunƙasa kasuwanci mai ɗorewa.
A yayin zaman tambayoyi da amsoshi, tawagar ta tattauna da jami’an Kano kan manufofin tattalin arziƙi, shirye-shiryen kasuwanci, jawo masu zuba jari da ƙirƙire-ƙirƙire.
Tawagar ta kuma yaba wa gwamnatin Kano bisa tarbar da aka yi mata, yayin da aka ce za ta ci gaba da ganawa da hukumomin gwamnati, ƙungiyoyi masu zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki a jihar.
