Daliba ta rasu bayan faɗowa daga bene mai hawa huɗu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wata ɗalibar Makarantar Koyon Aikin Shari’a ta Nijeriya mai shekara 23, Faith Alayande, ta rasu bayan ta faɗo daga saman ginin ɗakunan kwanan ɗalibai mai hawa huɗu a harabar makarantar da ke yankin Victoria Island a Jihar Legas.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas ta tabbatar cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Juma’a, 7 ga Agusta 2026.

Kakakin rundunar, Abimbola Adebisi, ta ce mai kula da ɗakunan kwanan ɗaliban ce ta sanar da ’yan sanda bayan an gano ɗalibar ba ta cikin hayyacinta a harabar makarantar.

A cewar Adebisi, wata ɗaliba da wani ɗan uwan marigayiyar sun gano wata wasiƙar yunƙurin kisan kai da ake zargin Alayande ta bari, sannan suka fara neman ta, amma ba su gan ta ba, kafin daga bisani aka gano cewa ɗalibar ta faɗo daga saman ginin ɗakunan kwanan ɗaliban.

Adebisi ta ce jami’an ’yan sanda sun isa wurin bayan mai kula da ɗakunan kwanan ɗaliban ta kai rahoton lamarin, inda suka ɗauke gawar marigayiyar zuwa ɗakin ajiye gawawwaki domin ci gaba da gudanar da bincike.

Wani mai sharhi kan harkokin tsaro, Zagazola Makama, wanda shi ma ya bayar da rahoton lamarin a shafinsa na ɗ, ya ce wata ɗaliba ce ta gano Alayande a harabar makarantar, sannan ta sanar da mai kula da ɗakunan kwanan ɗaliban.

Makama ya ce Babbar Mai Kula da ɗakunan kwanan ɗaliban Law School, Misis Igbokwe Juliana, ta kai rahoton lamarin Sashen ’Yan Sandan ɓictoria Island da misalin ƙarfe 6:30 na safe.

Ya ƙara da cewa binciken farko ya nuna cewa akwai yiwuwar ɗalibar ta faɗo daga saman ginin ɗakunan kwanan ɗaliban mai hawa huɗu.

Kakakin ’yan sandan ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano ainihin musabbabin rasuwar ɗalibar.

By ukarofi

Leave a Reply