Kwamishina ya yabi malaman tsangaya kan goyon bayan Inuwa da Jamilu gwamna a 2027

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe

Kwamishinan ƙananan hukumomi na Jihar Gombe, Barista Sani Ahmad Haruna, ya yaba wa malaman tsangaya na jihar bisa goyon bayan da suka bayyana wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya da ɗan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar APC, Dakta Jamilu Isiyaku Gwamna a zaɓen 2027.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne a zantawarsa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala wani babban taro da ƙungiyar malaman tsangaya ta jihar ta gudanar, inda malaman suka bayyana aniyarsu ta mara wa Dakta Jamilu Gwamna baya tare da tabbatar masa da ƙuri’u 150,000 a zaɓen 2027.

Ya ce matakin malaman na nuna godiya ne ga irin gudunmawar da gwamnatin Inuwa Yahaya ta bayar wajen farfaɗo da inganta ilimin Alƙur’ani da harkokin tsangaya a faɗin jihar.

A cewarsa, gwamnatin jihar ta gina manyan makarantun Tsangaya guda 11, ɗaya a kowace ƙaramar hukuma, tare da samar da cibiyoyin karatu da sauran abubuwan more rayuwa da suka taimaka wajen inganta tsarin karatun almajirai.

Barista Sani ya kuma buƙaci shugabannin ƙananan hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki su yi koyi da Gwamna Inuwa Yahaya wajen tallafa wa malaman tsangaya da sauran masu koyar da ilimin addini.

Malaman tsangaya da suka halarci taron sun ce goyon bayansu ga gwamnatin jihar ya samo asali ne daga irin tallafin da aka bai wa ilimin Alƙur’ani da jin daɗin almajirai.

Sun ce baya ga gina makarantu 11 na tsangaya, gwamnatin ta samar da cibiyoyin karatu sama da 120, tare da kayan karatu, masauki da shirye-shiryen koyar da ɗalibai sana’o’in dogaro da kai.

Malaman sun kuma yaba da shigar da almajirai 1,000 cikin tsarin inshorar lafiya na jihar, da kuma kafa hukumar almajiri, wadda suka ce za ta taimaka wajen samar da ingantaccen tsari na ci gaba da kula da ilimin Alƙur’ani.

Da take tsokaci babbar mai bai wa gwamna shawara kan Ilimin Almajiri da tsangaya, Sayyada Amina Sheikh Dahiru Bauchi, ta ce gwamnatin Inuwa Yahaya ta ba ilimin tsangaya muhimmanci ta hanyar haɗa ilimin addini da na zamani.

Ta ce an gina makarantun tsangaya 11 tare da kafa cibiyoyin horar da matasa, inda ake bai wa ɗalibai damar samun ilimi da sana’o’in dogaro da kai.

A cewarta, wasu daga cikin shirye-shiryen sun samo asali ne daga shirin BESDA, wanda ya samar da damammaki ga malaman Alƙur’ani da ɗalibai wajen samun ƙarin ilimi da dabarun dogaro da kai.

By ukarofi

Leave a Reply