Ma’aikatar kuɗi ta ɗora wa NNPCL laifin ɓatan bayanai yayin da majalisa ke binciken aron Dala 3bn da kuɗaɗen NLNG

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya ta ɗora wa Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL) laifi bisa rashin gabatar da rahotannin bayanan da ake buƙata don warware tambayoyin kuɗaɗe da aka yi a rahoton shirin tabbatar da gaskiya da adalci kan kuɗaɗen masana’antun fitarwa (NEITI) na mai da gas na 2021 zuwa 2023.

Babban Sakataren ma’aikatar, Raymond Omachi ne ya bayyana haka a ranar Alhamis yayin bayyana a gaban kwamitin binciken kuɗaɗen al’umma na Majalisar Dattawa, inda yake amsa tambayoyi kan rashin fahimtar haƙiƙanin yadda aka sarrafa wasu kuɗaɗe daga rahoton NEITI.

Daga cikin ababen da ake da matsala da su akwai Dala biliyan 3 na aro da aka karɓa gabanin shigo da mai zuwa Nijeriya a 2012 domin warware matsalolin biyan kuɗaɗen tallafi, waɗanda ba a fayyace yadda aka sanya su ba acikin asusun gudanarwa.

Rahoton ya kuma ƙalubalanci biyan Dala miliyan 722.6 daga Kamfanin Nigeria LNG Limited (NLNG) zuwa ga NNPC a 2021 a madadin gwamnati da aka samu daga kuɗaɗen ruwa da wasu kamusho.

A cewar NEITI, ba a tura kuɗaɗen ba ga asusun Tarayya ko kuma bayyana haƙiƙanin yadda aka yi da su.

Haka kuma, ma’aikatar ba ta bayar da amsa akan lokaci ba ga abin da NEITI ya gano cewa ga ɗaya daga cikin matatun mai na ƙasa da ke aiki duk da cewa an kashe sama da biliyan N200 akansu.

Da yake bayar da amsa, Raymond Omachi ya bayyana cewa, Ma’aikatar Kuɗi ba ta shiga hada-hadar kuɗaɗen da ake taƙaddama ba akansu kai-tsaye kuma matsalolin da aka samu a rahotannin kuɗaɗen daga hukumomin da ke da alhaki da su ne kai-tsaye musamman ma NNPCL.

Sakataren ya ƙara da cewa, akan haka ne ma’aikatar ta gayyaci wani kamfanin waje kan harkar rahotannin kuɗaɗe mai suna Arthur Anderson LLP da ya gudanar da rahoto na musamman kan kuɗaɗen tare da warware matsalolin da ake da ta damuwa akansu.

Saidai, kwamitin majalisar, wadda Sanata Ibrahim Ɗankwambo ke jagoranta, ya koka kan jinkirin rashin kammala rahoton akan lokaci bayan ma’aikatar kuɗin ta nemi a ƙara mata lokaci har sau biyu don kammala aikin, wato daga wata shida zuwa shekara guda.

Daga nan ne Omachi ya buƙaci wakilcin NNPCL da na Hukumar Gudanar da Harkokin Fetur ta Nijeriya (NUPRC) da su bayyana a gabanta kwamitin tare da ma’aikatar yayin bayar da bayanan da ake nazari akan nasu.

By Babaji

Leave a Reply