Adeleke ya zargi Oyetola da matsa wa EFCC ta rufe asusun Jihar Osun

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya zargi tsohon gwamnan jihar, Gboyega Oyetola, da kasancewa a bayan matakin da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta ɗauka na daskarar da asusun gwamnatin jihar.

Adeleke ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wani taron Arise Town Hall da aka shirya domin ’yan takarar kujerar gwamnan Jihar Osun, gabanin zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar ranar 15 ga Agusta.

Gwamnan ya yi zargin cewa Oyetola, wanda a yanzu yake riƙe da muƙamin Ministan Harkokin Ruwa da Tattalin Arziƙin Teku, yana amfani da sunan Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu wajen hulɗa da hukumomin gwamnatin tarayya domin matsa wa gwamnatinsa lamba.

Adeleke ya ce: “Na tabbata shi (Oyetola) ne ya gaya wa EFCC ta daskarar da asusunmu, cewa Shugaban ƙasa ne ya ce a daskarar da shi,” inji shi.

Sai dai gwamnan bai gabatar da wata hujja a wajen taron da za ta tabbatar da zargin cewa Oyetola ne ya umarci EFCC da ta ɗauki matakin daskarar da asusun jihar ba.

Adeleke ya kuma ce lamarin ya sauya bayan Shugaban ƙasa Tinubu ya tuntube shi da kansa kan batun.

Ya ce: “Saboda haka, lokacin da Shugaban ƙasa ya kira, mutane da dama sun yi mamaki. Lokacin da Shugaban ƙasa ya kira, ya ce abin ya ba shi kunya. Ya ce hakan ba abin karɓa ba ne, saboda na gaya masa cewa ba zai so dimokuraɗiyya ta durƙushe ba; yana son zaɓe na gaskiya da adalci.”

Gwamnan ya kuma zargi Oyetola da amfani da kusancinsa da Shugaban ƙasa wajen cimma muradun siyasa a Jihar Osun.

Adeleke ya ce Oyetola na fama da radadin shan kaye, yana mai zargin cewa yana amfani da ikon gwamnatin tarayya wajen matsa wa jihar lamba.

Ya ce: “Oyetola yana jin zafin shan kaye. Yana amfani da Shugaban ƙasa ne kawai wajen rantsuwar cewa zai lalata Jihar Osun. Yana amfani da ƙarfin gwamnatin tarayya,” inji Adeleke.

Adeleke da Oyetola sun kasance abokan hamayyar siyasa tun zaɓen gwamnan Jihar Osun na shekarar 2022, lokacin da Adeleke ya kayar da Oyetola, wanda a lokacin yake kan kujerar gwamna.

A yanzu dai Adeleke na neman wa’adi na biyu a matsayin gwamnan jihar a ƙarƙashin tutar jam’iyyar Accord Party, a zaɓen da za a gudanar ranar Asabar, 15 ga Agusta, 2026.

Zargin da Adeleke ya yi kan Oyetola ya kasance a matsayin zargi kawai, kuma babu wata shaida da aka gabatar a wajen taron da ta tabbatar da cewa Oyetola ne ya umarci EFCC ta daskarar da asusun gwamnatin Jihar Osun.

By ukarofi

Leave a Reply