Kaunar ƙasa ce ta sa na shirya juyin mulki kan Tinubu – Kanar Ma’aji

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kanar Mohammed Ma’aji na Rundunar Sojin Nijeriya, wanda ake zargi da jagorantar wani shirin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta hanyar juyin mulki, ya bayyana cewa abin da ya sa aka shirya shirin ba wata buƙata ta neman mulki ba ce, sai dai abin da ya kira kishin ƙasa da damuwa kan tabarbarewar tsaro da tattalin arzikin ƙasar.

An gano shirin ne a watan Satumba na 2025 kafin a aiwatar da shi, lamarin da ya haifar da kama da binciken jami’an soja masu ci da waɗanda suka yi ritaya, da kuma wasu fararen hula da ake zargi da hannu a shirin. Rundunar Sojin Nijeriya daga bisani ta tabbatar da cewa akwai wani zargi na shirin kifar da gwamnati, inda ta ce jami’an da aka samu da hannu za su fuskanci shari’ar soji.

Ma’aji, mai shekara 50, ya bayyana a cikin bayanan da ya bai wa masu bincike cewa tun daga shekarar 2023 ne aka fara tunanin shirin, a ƙarshen gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari. Ya ce matsalolin cin hanci da rashawa, nuna son kai, rashin tsaro, garkuwa da mutane da ayyukan ’yan bindiga, musamman a arewacin ƙasar, su ne suka fara haifar da tunanin cewa akwai buƙatar ɗaukar matakin soja.

A cewarsa, jami’an soji sun yi tsammanin manyan hafsoshin rundunar za su ɗauki matakin kawo ƙarshen matsalolin, amma hakan bai faru ba.

Ya ce wasu daga cikin jami’an da suka shiga shirin sun kasance masu kishin ƙasa da kuma burin ganin an samu sauyi mai kyau a ƙasar.

Ma’aji ya bayyana cewa rashin kuɗi, kayan aiki da isassun jami’an da za su shiga shirin ya sa ba a samu damar aiwatar da shi a farkon lokacin ba. Ya ce mafi yawan kuɗin da aka kashe a lokacin sun fito ne daga aljihunsa, ciki har da kuɗin da ya samu daga sayar da kadarorinsa.

Ya ce ya sayar da gidaje uku a Jihar Kaduna da wani gidan kwanan ɗalibai da ke Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya domin tallafa wa shirin. Ya kuma bayyana cewa wani jami’i ya bayar da Naira miliyan ɗaya, yayin da wani ya bayar da gudummawa da kuɗin ƙasashen waje.

Ma’aji ya ce shirin ya sake farfaɗowa ne bayan da ya gaza samun nasarar cin jarabawar ɗaukaka shi zuwa matsayin Birgediya Janar a karo na biyu a shekarar 2024.

A cewarsa, wasu jami’ai sun nuna damuwa cewa ana iya yi masa ritaya daga aikin soja, inda suka matsa masa ya farfaɗo da shirin. Ya ce Laftanar Kanar Shamsuddeen Bappah na daga cikin jami’an da suka matsa masa lamba sosai kan hakan.

Ya ce daga ƙarshen 2024 zuwa farkon 2025 aka fara gudanar da wasu taruka a wurare daban-daban a Abuja, inda wasu daga cikin jami’an suka ci gaba da halarta, yayin da wasu sabbin mutane suka shiga.

Kanar Ma’aji ya musanta cewa gazawarsa wajen samun ɗaukaka matsayi ce babban abin da ya sa ya shiga shirin. Ya ce matsalolin da ƙasar ke fuskanta ƙarƙashin gwamnatin Tinubu sun ƙara tsananta a ra’ayinsu.

Ya kawo cire tallafin man fetur, sauya tsarin canjin kuɗin Naira, ƙarin haraji, ƙarin kuɗin wutar lantarki, cin hanci da rashawa da kuma rashin tsaro a matsayin wasu daga cikin abubuwan da suka ƙara musu damuwa.

Ya kuma ambaci zanga-zangar #EndSARS, #EndBadGoɓernance da Take Back Your Country, yana mai cewa ƙoƙarin matasa na ganin shugabanni sun saurari koken da suke yi bai haifar da sakamakon da suke so ba.

A cewarsa, amfani da ƙarfi da jami’an tsaro suka yi wajen dakile wasu daga cikin zanga-zangar ya ƙara haifar da takaici a tsakanin matasa.

Ma’aji ya ce matasan Nijeriya da dama suna cikin rashin aikin yi, takaici da rashin tabbas game da makomarsu. Ya kuma bayyana damuwarsa kan halin da tsofaffin sojoji da waɗanda suka yi ritaya ke ciki, yana mai cewa wasu daga cikinsu sun sha wahala kafin su samu hakkokinsu na fansho da sauran alawus-alawus.

Ya ce shi ma yana fuskantar matsalar tattalin arziki wajen kula da ’ya’yansa biyar da albashinsa, yana mai tambayar yadda talakawan soji za su iya biyan kuɗin makaranta da sauran bukatun iyalansu a cikin tsadar rayuwa.

Ya kuma nuna damuwa kan yadda ake kula da sojojin da suka samu raunuka a lokacin yaƙi, musamman a Asibitin Sojoji na 44 da ke Kaduna.

A cewarsa, waɗannan matsaloli ne suka ƙarfafa imaninsa cewa ƙasar na tafiya zuwa wani yanayi mai haɗari.

Ma’aji ya jaddada cewa abin da ya kira “kishin ƙasa” ne ya sa aka fara tunanin ɗaukar matakin soja, yana mai cewa manufar ita ce a samar da ƙasa mai wadata wadda ’yan ƙasa za su yi alfahari da ita.

Sai dai ya bayyana cewa bai kai ga samun cikakken tsarin gudanar da shirin ba, kuma ba a tsara wata ranar aiwatar da shi, wato “D-Day”, ba.

Wasu bayanan da ke cikin takardun binciken sun shafi zargin yadda aka shirya tattara jami’ai, sadarwa, makamai da kuma matakan da ake son ɗauka kan wasu manyan jami’an gwamnati da sojoji. Sai dai waɗannan zarge-zarge na gaban kotu ne kuma ba su tabbatar da cewa an aiwatar da wani juyin mulki ba.

Haka kuma, Ma’aji ya musanta cewa wasu manyan jami’an soja da aka danganta da shirin suna da hannu, yana mai cewa wasu daga cikin jami’an sun san damuwar da ke tsakanin sojoji ne kawai, ba wai sun shiga cikin shirin ba.

Tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa, Timipre Sylɓa, wanda aka zarga da kasancewa ɗaya daga cikin masu ɗaukar nauyin shirin, ya musanta duk wata alaƙa da zargin juyin mulkin.

Sylɓa, wanda ya taɓa zama ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur a gwamnatin Buhari, ya bayyana kansa a matsayin cikakken ɗan dimokuraɗiyya, yana mai cewa ba shi da wata alaƙa da shirin, ko wajen tsara shi ko kuma samar da kuɗaɗen gudanar da shi.

A nasa bayanin, Ma’aji ya gabatar da shawarwari da dama da ya ce za su taimaka wajen hana sake faruwar irin wannan lamari.

Ya yi kira da a ƙara albashin jami’an Sojin Nijeriya tare da inganta jin daɗinsu da na iyalansu. Ya kuma buƙaci a inganta kula da sojojin da suka samu raunuka, a faɗaɗa shirin rancen COAS, a sake duba tsarin inshorar lafiya na sojoji, da kuma samar da shirye-shiryen gidaje masu ɗorewa ga jami’an soja.

Ya kuma yi kira da a farfaɗo da shirye-shiryen ba jami’an soja rancen sayen motoci tare da kafa wani sashe na musamman da zai mayar da hankali kan jin daɗin ma’aikatan rundunar.

Kan batun abin da ya kira “godfatherism” a cikin rundunar soja, Ma’aji ya yi suka kan tsarin da wasu jami’ai ke ganin cewa sai sun samu goyon bayan masu faɗa a ji kafin su samu ci gaba a aiki.

Ya kuma nemi a inganta fansho da sauran hakkokin tsofaffin jami’an soja, yana mai cewa waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen kare ƙasa sun cancanci kulawa mai kyau.

Game da cire tallafin man fetur, Ma’aji ya ce kamata ya yi a aiwatar da matakin a hankali, maimakon yin hakan cikin gaggawa. Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta zuba kuɗin da aka samu daga cire tallafin wajen ayyukan da za su rage wa ’yan ƙasa wahala.

Ya ƙara yin kira da a ƙara yaƙi da cin hanci da rashawa, tare da inganta harkar ilimi da rage matsalolin da suka shafi kasafin kuɗi.

Ma’aji ya kuma buƙaci a kafa wata hanya ta sadarwa ta musamman da za ta bai wa jami’an soja damar kai koke-kokensu kai tsaye ga Babban Hafsan Sojin ƙasa ba tare da tsoron fuskantar ramuwar gayya ba.

A ƙarshen bayaninsa, Ma’aji ya ce zaman da ya yi a tsare da kuma binciken da aka gudanar a kansa ya sauya fahimtarsa. Ya ce idan aka sake shi kuma matsalolin da suka haifar da lamarin suka ci gaba, zai iya tunanin “wata hanya dabam”, amma ya ƙara da cewa hulɗarsa da kwamitin binciken ta nuna masa cewa akwai wasu hanyoyin bayyana damuwa ba tare da ɗaukar matakin juyin mulki ba.

Ya roƙi hukumomi da su yafe masa tare da yi masa sassauci, yana mai cewa zargin shirin bai kai ga cutar da wani mutum ko harbin ko da harsashi ɗaya ba.

“Idan Allah Ya yarda, idan hukumomi suka yi mana afuwa, ba za mu sake tunanin ɗaukar wannan hanya ba a nan gaba,” inji shi.

A halin yanzu, Ma’aji da sauran jami’an da ake tuhuma suna fuskantar shari’a a gaban Kotun Soji, inda suka musanta aikata laifin da ake zarginsu da shi.

Haka kuma, wasu mutane shida da suka haɗa da tsofaffin jami’an soja suna fuskantar shari’a a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan zargin da ya shafi wannan batu. Su ma sun musanta aikata laifin tare da ƙalubalantar sahihancin wasu daga cikin bayanan da aka samu yayin binciken.

ƙarar tana ci gaba da kasancewa a gaban kotuna, kuma zarge-zargen da ke cikin bayanan Ma’aji da sauran waɗanda aka yi wa tambayoyi ba su kasance hujjar tabbatar da laifi ba. Kotuna ne za su yanke hukunci kan laifi ko rashin laifi bayan sun duba dukkan hujjojin da ɓangarorin biyu suka gabatar.

By ukarofi