A Ringim shekaru 50 al’umma na fama da matsalolin lafiya — Garba Dabi

Spread the love

Daga ABDULLAHI SANI DOGUWA a Kano

Shugaban ƙaramar Hukumar Ringim ta Jihar Jigawa, Hon. Badamasi Garba Dabi, ya bayyana cewa al’ummar yankin sun shafe kusan shekaru 50 suna fama da matsaloli a fannin kiwon lafiya, kafin zuwansa shugabancin ƙaramar hukumar.

Da yake jawabi ga manema labarai a ofishinsa da ke Sakatariyar ƙaramar Hukumar Ringim, Hon. Badamasi Garba Dabi ya ce tun bayan da Allah (A.W.T) Ya ɗora masa nauyin jagorantar al’ummar yankin, ya mayar da hankali wajen sauraron koke-kokensu da kuma nemo hanyoyin magance matsalolin da suka daɗe suna addabar su.

Ya ce daga cikin muhimman fannoni da ya ba fifiko akwai harkar lafiya, wadda ya bayyana a matsayin ginshiƙin ci gaban rayuwar ɗan Adam, da kuma ilimi, wanda shi ma yake daga cikin abubuwan da suka fi muhimmanci ga ci gaban al’umma.

A cewarsa, shugabancinsa ya yi ƙoƙari wajen bayar da agajin da ya dace a fannin kiwon lafiya, inda aka samar da babban Asibitin Ringim mai ɗauke da kayan aiki da tsarin zamani, da nufin sauƙaƙa wa al’umma, musamman talakawa, samun kulawar lafiya.

Ya ƙara da cewa an kuma samar da wani asibiti na musamman a wani yanki da ake kira Gidan Maza, wanda ya ce zai taimaka wajen kula da nau’o’in marasa lafiya daban-daban.

Dabi ya ce ƙaramar Hukumar Ringim kan ware wani kaso na kuɗaɗenta domin sayen magunguna da rabawa ga al’ummar ƙaramar hukumar, musamman ƙananan yara, mata masu juna biyu da sauran marasa ƙarfi.

Hon. Badamasi Garba Dabi ya bayyana cewa ɗaukar waɗannan matakai ya biyo bayan fahimtar matsalar da al’ummar yankin suka shafe shekaru masu yawa suna fuskanta a fannin lafiya, lamarin da ya ce ya kusa mayar da yankin baya wajen samun ingantacciyar kulawar lafiya.

Ya ce lokacin da ya karɓi shugabancin ƙaramar hukumar, ya tarar da ita cikin wani yanayi marar kyau, inda ma’aikatan lafiya da ma’aikatan majalisar ƙaramar hukumar ke fuskantar matsaloli wajen gudanar da ayyukansu saboda rashin kyakkyawan yanayin aiki da kuma wasu matsalolin da suka shafi walwalar ma’aikata.

Dabi ya ce ya yi ƙoƙarin sauya wannan yanayi, inda yanzu harkokin ƙaramar hukumar ke tafiya yadda ya kamata, bisa tsare-tsaren da aka tsara a ƙarƙashin tsarin gwamnatin Jihar Jigawa, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Umar A. Namadi, musamman a fannin ilimi da sauran manufofin gwamnati na inganta rayuwar al’umma.

A cewarsa, wannan ne ya sa ƙaramar hukumar ta ɗauki nauyin tallafa wa marasa galihu da ke cikin al’umma, tare da mayar da hankali kan ilimi, raya karkara, musamman yankunan da ke fuskantar matsalar rashin ruwa da magudanan ruwa.

Ya ce ƙaramar hukumar ta kuma shiga aikin gyaran wasu masallatai, musamman na Kamsal Salawati, domin samar da yanayi mai kyau ga al’ummar Musulmi wajen gudanar da ibadunsu, musamman a lokacin damina.

Baya ga haka, ya ce an kuma kula da wasu wuraren da yara da dama ke karatun Alƙur’ani mai girma, inda aka fuskanci matsalar rashin ingantattun wuraren zama. Ya ce ƙaramar hukumar ta yi ƙoƙari wajen gyara irin waɗannan wurare tare da ɗaukar nauyin wasu malamai.

Haka nan, Hon. Badamasi Garba Dabi ya ce ƙaramar hukumar ta samu nasarar shawo kan matsalar cushewar magudanan ruwa da ke haifar da ambaliyar ruwa a wasu sassan garin Ringim.

Ya ba da misali da wasu unguwanni da ke cikin ƙwarin garin Ringim, musamman unguwar Nassarawa, inda ya ce a baya, duk lokacin da aka yi ruwa, mazauna wasu unguwanni kan fuskanci matsalar rashin samun damar shiga ko fita daga gidajensu sakamakon ambaliyar ruwa.

Ya ce irin wannan matsala ta kuma shafi mahaifarsa ta Dabi, sakamakon cushewar magudanan ruwa, lamarin da ya ce ƙaramar hukumar ta riga ta magance.

Dangane da batun ruwan sha kuwa, Hon. Badamasi Garba Dabi ya ce a halin yanzu babu wata babbar matsala da al’ummar yankin ke fuskanta wajen samun ruwan sha.

Da ya juya kan matsalar rashin fahimtar juna tsakanin Fulani makiyaya da manoma, musamman a wasu yankunan da ke maƙwabtaka da ƙaramar Hukumar Ringim, Dabi ya ce duk da cewa Allah ba Ya ɗora wa bawa abin da ba zai iya ba, akwai buƙatar a ɗauki matakan da za su hana rikice-rikice faruwa.

A matsayinsa na manomi kuma ɗan asalin Fulani, ya ce yana da cikakken fahimtar yadda rikice-rikicen da ke faruwa tsakanin Fulani makiyaya da manoma ke iya haifar da matsaloli ga zaman lafiya da ci gaban al’umma.

Saboda haka, ya ce ƙaramar Hukumar Ringim ta ga dacewar haɗa ƙungiyoyin Fulani da shugabannin manoma na yankin domin tattauna hanyoyin magance matsalolin da ka iya haifar da rikici tare da kare zaman lafiya a yankin.

Ya ce gwamnatin Jihar Jigawa, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Umar A. Namadi, ta riga ta gudanar da zama da shugabannin ƙungiyoyin biyu domin neman haɗin kansu da amincewarsu wajen tabbatar da ɗorewar zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya.

Kazalika, Hon. Badamasi Garba Dabi ya yi ƙarin haske kan batun katin zaɓe na dindindin (PVC), inda ya buƙaci al’ummar yankin da su tabbatar sun mallaki katin zaɓensu tare da sabunta shi a lokacin da ya dace.

Daga bisani, ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga al’ummar ƙaramar Hukumar Ringim da su ci gaba da yawaita addu’o’in fatan alheri ga shugabancin ƙaramar hukumar da Jihar Jigawa baki ɗaya, domin samun damar sauke nauyin da ke kansu na yi wa al’umma hidima.

By ukarofi

Leave a Reply