Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Jam’iyyar All Progressives Congress APC reshen jihar Zamfara ta zargi Hon. Aminu Sani Jaji da yin zagon ƙasa ga gwamnatin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da yin adawa da jam’iyyar inda ya kafa jam’iyyar APC mai kama da juna a jihar Zamfara.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na jihar Yusuf Idris a Gusau ranar Talata.
Jam’iyyar ta zargi Hon Aminu Sani Jaji da yin wani yunƙuri na ɓata wa shugabannin jam’iyyar a ƙarƙashin Alh. Tukur ɗanfulani suna, yayin da ta bayyana matakin nasa a matsayin saɓa wa dokar da rashin bin tsarin dimokraɗiyya.
Jam’iyyar ta kuma ƙalubalanci Hon Aminu Sani Jaji kan ayyana Mansur Khalifa da Isiaka Ajiya Anka a matsayin sakataren jam’iyyar APC na jiha da kuma shugaban jam’iyyar a jihar ta Zamfara.
Hakazalika jam’iyyar ta ƙara zargin Hon. Aminu Sani Jaji da jama’ar sa kan zagin shugabanni da nuna cewar yana tare da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, tana mai cewa hakan baya nuna mutunta jam’iyya da shugabanni musamman a lokacin da Jaji ke iƙirarin cewa shi ne ya ɗauki nauyin yaƙin neman zaɓen Tinubu a yankin Arewa maso Yamma a 2023 da Naira biliyan 20.
Jam’iyyar ta bayyana shugabannin jam’iyyar APC a ƙarƙashin Hon. Aminu Sani Jaji a jihar Zamfara a matsayin haramtattun jagororin APC na Zamfara.
“Jam’iyyar a ƙarƙashin Hon. Tukur Umar ɗanfulani a shirye take ta tunkari duk wani dan siyasa da ke ƙoƙarin haifar da matsala ga jam’iyyarmu da shugabanninta a dukkan matakai.”
“Muna jaddada ƙudirin jam’iyyar mu na goyon bayan sabon ajandar kawo sayi da Shugaba Bola Tinubu yake yi da kuma dukkan shugabannin jihohin da ake girmamawa,” sanarwar ta bayyana.
Blueprint Manhaja ta tattaro cewa Hon. Aminu Sani Jaji mamba ne mai wakiltar ƙananan hukumomin Birnin Magaji da ƙaura Namoda a jihar Zamfara a majalisar wakilai ta tarayya ƙarƙashin
