NAHCON ta sanya farashin kujerar Hajjin 2027 da ranar rufewa

Spread the love

Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya NAHCON, ta sanar da adadin farashin kujerar aikin Hajjin 2027 da aka amince da su, waɗanda suka fara daga Naira miliyan 7.56 zuwa miliyan N7.88, bisa la’akari da yankin da mahajjata za su tashi.

A sanarwar da NAHCON ta fitar a ranarJuma’a, ta ce Gwamnatin Tarayya ta amince da kudaden ne bayan tattaunawa da Ƙungiyar Hukumomin Jin Daɗin Alhazai na Jihohi da kamfanonin jigilar alhazai na Saudiyya, tare da la’akari da farashin canjin kuɗi da kuma halin da farashin ayyuka ke ciki.

A ƙarƙashin sabon tsarin kudaden, maniyyatan da za su tashi daga yankin Maiduguri/Yola za su biya Naira miliyan 7,560,822; waɗanda za su tashi daga yankin Arewa za su biya Naira miliyan 7,672,822; yayin da maniyyaran da za su tashi daga yankin Kudu za su biya Naira miliyan 7,882,822.

NAHCON ta ce maniyyatan da suka riga suka biya kuɗin farko na Naira miliyan 5 ana buƙatar su biya sauran kuɗin da ya rage domin kammala rajistarsu.

Sabbin masu rajista kuma za su biya kuɗin ne ta hukumomin jin daɗin alhazai ko kwamitocin kula da aikin Hajji na jihohinsu, ko kuma bankunan da aka amince da su waɗanda ke cikin shirin ajiyar kuɗin Hajji.

Hukumar ta kuma sanya 26 ga Satumba, 2026 a matsayin wa’adin ƙarshe na kammala ɗora bayanan yatsun hannu da sauran bayanan ƙwayoyin halitta na duk masu niyyar zuwa Hajji a dandalin Nusuk-Masar.

Haka kuma, ta umarci jihohi da su kammala tura dukkan kuɗaɗen Hajjin 2027 zuwa 2 ga Disamba, 2026, tana mai gargaɗin cewa ba za a ƙara wa’adin ba.

Kazalika, NAHCON ta ce rashin cika waɗannan wa’adoji ka iya haifar da soke guraben Hajjin da aka ware wa jihohin.

By Babaji

Leave a Reply