Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban Kamfanin Jirgin Sama na Air Peace, Allen Onyema, ya yi gargaɗin cewa, masana’antar sufurin jiragen sama ta Nijeriya na fuskantar yanayi na barazana, yana mai cewa wasu kamfanonin jiragen saman cikin gida na iya durƙushewa cikin kwanaki 30 masu zuwa matuƙar ba a ɗauki matakan gaggawa wajen magance matsalolin da ke addabar masu gudanar da harkar ba.
Onyema ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai a wajen ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar Shugaban Kamfanin Jiragen Sama na Med-View, Muneer Bankole, mai suna Pathways, Pilgrimage and Destiny.
Shugaban Air Peace ya ce taƙaddamar da ta taso kan yadda ake biyan Kuɗin Kashi Biyar na Tikitin Jirgin Sama da Kayayyakin Da Aka Sayar (TSC) ba ta samo asali ne daga ƙin biyan kuɗaɗen da doka ta tanada da kamfanonin jiragen sama suka yi ba, sai dai nauyin da tsarin karɓar kuɗin ke ɗora musu.
Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da masu gudanar da kamfanonin jiragen sama da su zauna su tattauna cikin fahimta domin samar da ingantaccen tsarin karɓar kuɗaɗen, yana ba da shawarar a maye gurbin tsarin da ake da shi da tsayayyen kuɗin da za a dinga caji kan kowane tikiti ko kaya, wanda zai kawar da taƙaddamar da ke tasowa kan abubuwan da ya kamata a haɗa cikin kuɗin jirgin wajen ƙididdige harajin.
Onyema ya kuma yi Allah-wadai da barazanar da ƙungiyoyin ƙwadago suka yi na gudanar da zanga-zangar toshe ayyukan kamfanonin jiragen sama saboda taƙaddamar, yana mai bayyana matakin a matsayin abin da ba a saba gani ba kuma wani yunƙuri na tsoratar da masu gudanar da kamfanonin jiragen sama.
Ya ce, kamfanonin jiragen sama sun daɗe suna tattaunawa da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Nijeriya (NCAA) da Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama ta Tarayya, yana mai jaddada cewa masana’antar ba ta cikin wata taƙaddama da ƙungiyoyin ƙwadago.
A cewarsa, kamfanonin jiragen saman Nijeriya na gudanar da ayyukansu cikin yanayi mai tsananin wahala, sakamakon tsadar rancen kuɗi, ƙarancin kayayyakin more rayuwa, yawan haɗuwar jirage da tsuntsaye da kuma ɗimbin kuɗaɗen gudanar da ayyuka da ake karɓa daga kamfanonin.
Onyema ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta shiga tsakani domin daƙile sake durƙushewar wasu kamfanonin jiragen sama, yana mai cewa fiye da kamfanonin jiragen sama 50 na Najeriya sun rufe ayyukansu tsawon shekaru, duk da cewa wasu daga cikin masu kamfanonin sun yi nasara a wasu fannoni na kasuwanci.
Sai dai ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da nuna goyon baya ga kamfanonin jiragen sama na cikin gida, kuma ba zai bari masana’antar sufurin jiragen sama ta Nijeriya ta durƙushe ba.
Shugaban Air Peace ya yi kira da a samar da manufofin da za su ƙarfafa kamfanonin jiragen saman cikin gida maimakon raunana su, yana mai cewa hakan na da muhimmanci wajen tabbatar da ɗorewar masana’antar sufurin jiragen sama da kuma tsira da makomar harkar a Nijeriya.
