Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe
Ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa reshen jihar Gombe, NBA, ta bayyana jigo tare da kaddamar da tambarin makon shari’a na shekarar 2026, yayin da manyan lauyoyi suka nuna goyon bayansu ta hanyar bayar da gudummawar kuɗi da kuma alƙawarin tallafawa shirin.
Da yake jawabi a wajen taron ƙaddamarwar da aka gudanar a Gombe, shugaban ƙungiyar NBA na reshen Gombe, Barrista Alhassan Mu’azu, ya bayyana cewa taron ya samu halartar sama da mutum 500 da suka haɗa da lauyoyi, ‘yan jarida da sauran masu ruwa da tsaki a ɓangaren shari’a.
Ya ce jigon makon shari’ar na shekarar 2026 mai taken “ƙarfafa G’gyaran tsarin shari’a: Lauyoyi a Matsayin wakilan sauyi” an zaɓe shi ne domin jaddada muhimmiyar rawar da lauyoyi ke takawa wajen inganta gyare-gyare da kuma ƙarfafa tsarin shari’a a ƙasa.
A cewarsa, rashin adalci na daga cikin abubuwan da kan haddasa rashin zaman lafiya da rikice-rikice a cikin al’umma, don haka ya buƙaci lauyoyi da sauran masu ruwa da tsaki su haɗa kai domin tabbatar da gaskiya, adalci da riƙon amana a tsarin shari’a.
Ya ce: “Wannan jigo yana da matukar muhimmanci domin yana mayar da hankali kan buƙatar gyare-gyare a ɓangaren shari’a. Ba lauyoyi kaɗai abin ya shafa ba, har da ɓangaren shari’a gaba ɗaya da sauran masu ruwa da tsaki.
“Burinmu shi ne mu tabbatar cewa tsarin shari’a yana aiki ga kowa da kowa, mai kuɗi ko talaka, mai ilimi ko marar ilimi.”
Ita ma da take jawabi, shugabar kwamitin shirya makon shari’ar, Barrista Hannatu Dauda Simon, ta ce ƙaddamar da tambarin makon shari’ar na nuna ƙudurin ƙungiyar wajen kare adalci, ƙwarewa da kuma ingantaccen aiki a harkar lauya.
Ta bayyana cewa makon shari’ar zai zama wata dama ta wayar da kan lauyoyi da jama’a kan muhimmancin bin dokokin ƙasa da kuma inganta samun adalci ga kowa da kowa.
Barrista Hannatu ta kara da cewa za a fara gudanar da ayyukan Makon Shari’ar a ranar 15 ga Mayu, 2026 da ziyarar gidan yari tare da Sallar Juma’a ta musamman, sannan a bi da hidimar coci a ranar 17 ga Mayu.
Ta ce manyan shirye-shiryen Makon Shari’ar za su gudana daga Litinin 18 zuwa Alhamis 21 ga Mayu, inda za a gudanar da taron buɗe shirin, tattaunawar haɗin gwiwa tsakanin lauyoyi, alƙalai da ‘yan majalisa, da kuma gabatar da muhimman darussa daga ƙwararru a fannin shari’a.
A cewarta, ana sa ran manyan masana da ƙwararru a harkar shari’a za su halarci taron domin gabatar da jawabai kan muhimman batutuwan da suka shafi ɓangaren shari’a.
Daga cikin waɗanda ake sa ran za su halarta akwai Barrista Dele Adesina (SAN) a matsayin babban mai gabatar da jawabi, Barrista Festus Keyamo (SAN), Ministan Sufurin Jiragen Sama a matsayin babban baƙo na musamman, sai Farfesa M. T. Ladan na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Farfesa David Agbu, da kuma Barrista I. M. Attahir, ɗaya daga cikin manyan lauyoyin Gombe.
A yayin taron, Barrista Haruna Luka ya bayar da gudummawar Naira miliyan ɗaya domin tallafa wa gudanar da Makon Shari’ar, yayin da wasu lauyoyi da dama suka yi alƙawarin bayar da tallafi domin tabbatar da nasarar shirin.
A saƙon fatan alherinta, shugabar ƙungiyar lauyoyin mata ta duniya (FIDA) a jihar Gombe, Barrista Tala’atu Abubakar, ta buƙaci mambobin ƙungiyar da su gaggauta biyan kuɗin rajista tare da halartar dukkan ayyukan da aka shirya gudanarwa a lokacin makon shari’ar.
