Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Ƙungiyar Rasulul A’azam Foundation (RAAF), wacce ta ƙunshi mabiya Ahlul Baiti na gidan Manzon Allah (S.A.W.)wanda aka fi sani ƴan shi’a mai hedkwata a Kano, ta kai ziyara ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, inda ta gabatar da muhimman ƙorafe-ƙorafe da kuma buƙatu dangane da shirin muƙabalar da Majalisar Shura ta Jihar Kano za ta shirya da Malam Lawan Triumph.
A yayin ziyarar a yau Alhamis, shugaban ɓangaren tabligh na ƙungiyar, Sheikh Bashir Lawan Kano, ya bayyana cewa RAAF na neman a saka ta cikin mahalarta muƙabalar, kasancewar tana da tasiri da muhimmiyar rawa wajen isar da saƙon addini a jihar Kano.
Sheikh Bashir ya nuna ƙorafi kan yadda ake mai da mabiya Shi’a saniyar ware a harkokin gudanar da mulki da shari’ar addini a jihar, yana mai cewa hakan ba zai taimaka wajen gina zaman lafiya da haɗin kai ba.
Ƙungiyar ta kuma yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da hukunta Malam Lawan bisa zarge-zargen da ake yi masa mara sa daɗi ga fiyayyen halitta, tare da roƙon a bar kotu ta ci gaba da gudanar da shari’ar da ake yi wa Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ba tare da katsalandan daga ɓangarorin siyasa ko gwamnati ba.
Bugu da ƙari, shugaban ƙungiyar ya zargi tsohuwar gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje da nuna ɓangaranci tsakanin ƙungiyoyin addini a jihar, yana mai cewa hakan ne ya jefa al’amuran addini cikin rashin daidaito.
Kazalika, Sheikh Bashir Lawan ya kuma jaddada cewa mabiya Shi’a sun taka muhimmiyar rawa wajen samar da gwamnatin jihar Kano a zaɓen da ya gabata, don haka su ma na da haƙƙin a mutunta su da kuma ba su gurbi a manyan guraben da ake bai wa kowanne ƙungiyoyin addini da ma siyasa.
Daga nan ƙungiyar ta yi kira ga gwamnatin Kano da ta tabbatar da gaskiya da adalci a tsakanin dukkan mazahabobi, domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
