Rasuwar Marubuciya Hauwa Ƙamshi ta girgiza duniyar marubuta Hausa

Spread the love

Daga AISHA ASAS

A jiya ne aka wayi gari duniyar marubuta Hausa ta girgiza sakamakon rasuwar ɗaya daga cikin fitattun marubuta mata, Hauwa Abubakar Lawal Maiturare, wacce ake kira da ƙamshi bayan gajeriyar rashin lafiya. 

Hauwa ƙamshi ta rasu ne bayan ‘yan uwa da abokan arziki sun yi mata rakita zuwa sabon gidan da ta gina kuma ta tare a ranar Laraba,

inda majiyar Blueprint Manhaja ta shaida mana cewa, a maraicen ranar ne ta yi ƙorafin kanta da jikinta na ciwo, don haka ta buƙaci ta kwanta ta ɗan huta.

Bayan kwanciyar dai sai jikin ya rikice. Nan da nan aka garzaya zuwa asibiti, amma kafin a je rai ya yi halinsa.

Marubuci Kabiru Yusuf Fagge, wanda ake kira da Anka, ya wallafa bayani kan rayuwar Hauwa ƙamshi jim kaɗan bayan rasuwarta.

Rayuwar Marubuciya Hauwa Abubakar Lawal Maiturare (Ƙamshi):

An haifi Hauwa a unguwar Dala, ta cikin Kano. Tun tana ƙarama ta fara zuwa makaranatar allo da ɗaukar karatun Muhammadiyya.

Hauwa ta yi karatun firamare a Yalwa Primary School, ta fara karatun sakandire a makarantar yar Kawu wato GGSS Kawu, bayan shekara ɗaya aka mayar da ita GGC Dala, duk dai a Kano. Ba ta daɗe ba a GGC Dala ba, rashin uba ya riske ta, marubuciyar tana aji huɗu na sakandire aka yi mata aure. Ta ƙarasa karatun sakandire a ɗakin mijinta.

Bayan ta kammala, sai ta samu gurbin ci gaba da karatun ta a FCG Kano inda ta samu NCE. Bayan shekara ɗaya Hauwa ta samu aiki a Kano State Teachers Service Board, a matsayin malamar makaranta.

Bayan shekaru marubuciyar ta samu damar ci gaba da karatu a Jamiar Bayero da ke Kano, a Sashen Koyar da Harsunan Najeriya, inda ta yi digiri na ɗaya da na biyu.

Hauwa ta yi saukar karatun Alƙur’ani a gidan mijinta. Allah ya albarkaci Hauwa da ‘ya’ya biyar.

Babban abin da ya bai wa Hauwa sha’awar shiga harkar rubutu, shi ne yawan karance-karance da ta fara daga bisani domin ko a lokacin ƙuruciyarta ba ta da sha’awar karance-karance sai da zaman kaɗaici ya riske ta, ta fara ɗaukan littattafan Hausa tana karantawa inda har ta tsinci kanta da yi wa marubutan gyare-gyare a rubutunsu, har tana bai wa maigida labari. 

A haka ne maigida ya ba ta shawarar ita ma ta fara rubutu. Sai kuma shawarar sa ta zauna mata a zuciya. Ta fara rubuta littafin ‘Da Na Sani’ amma Allah bai bada sa’ar fitar da shi ba. 

A taƙaice dai fitilar magabata ta haska wa Hauwa sha’awar fara rubutu. Wannan sha’awar ce ta sa Hauwa ta fara karatun harshen Hausa a jami’a.

Rubutun Hauwa ya fi haskaka gidajen al’umma musamman mata kasancewar ‘ya mace ita ce tushen al’umma

Marubuciyar ta fara rubutu a cikin shekarar 1998. Ga jerin littattafanta:

-Khairiyya 

-Biyayya

-Babbar Mace

-Jarrabin rayuwa

-Rikita-rikitan Zamani

-ƙwai Tara Tsinana

-Haske Maganin Duhu

-Ita ce Sila

-Kundin ƙaddara

-Abun Dunƙule

Babban fatan Hauwa Maiturare ga rayuwar ‘ya’ya mata shi ne zaman su lafiya da yin rayuwa mai nagarta da inganci. Tana da burika kamar:

-Mata su nemi ilimi don inganta rayuwar al’umma.

-Da yin sana’o’i don dogaro da kai da tallafawa iyali.

-Tana da burin ganin ingantar harkar rubuce-rubucen Hausa.

Hauwa ta tsunduma fagen yabon Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam.

Marubuciya Hauwa Lawan Maiturare ta koma ga ubangijinta a ranar Alhamis, 1 ga Oktoba. Allah ya gafarta mata, Amin.

By ukarofi