Ɓangaren Gwamna Makinde ya naɗa Kabiru Turaki a matsayin shugaban riƙo na PDP

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ɓangaren jam’iyyar PDP da ke goyon bayan Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya sanar da naɗa Kabiru Tanimu Turaki a matsayin shugaban riƙon ƙwarya na ƙasa na jam’iyyar.

An naɗa Turaki ne domin jagorantar kwamitin riƙo mai mambobi 13 a ranar Litinin, yayin taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) karo na 103 da aka gudanar a Abuja, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin shugabanci ke addabar jam’iyyar a mataki na ƙasa.

By Babaji