Tare da SHAMSIYYA USMAN MANGA
Ɓarin ciki:
Shi ne zubewar ciki kafin ɗan tayi ko jariri ya zama cikakkiyar hallita a cikin mahaifa. Yawanci yana faruwa ne kafin ciki ya kai sati 20. Wani lokacin yana faruwa a bisa tsautsayi ko akasi, wani lokacin kuma yana faruwa bayan an shirya faruwar hakan.
Aƙalla ana samun kaso miliyan 73 na ɓarewar cikin da ƙirƙirar shi a kowace shekara a faɗin duniya (Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO – 2020). Kaso 40 daga ciki yana zama marar tsafta, musamman a wajajen da suke da ƙarancin kayan aiki. Irin haka yana taimakawa wajen haifar da mutuwar iyaye da kaso 13 a duniya.
Ire-iren ɓarin ciki:
1. ɓarin da ya auku bisa akasi:
Shi wannan yawancin yana faruwa ne kwatsam ba tare da an shirya ko an so ba.
Shi ma a ƙasan shi akwai kashe-kashe kamar haka:
a. Cikin da yake zubar da jini, amma kuma bakin mahaifa bai buɗe ba. Abin da wannan yake buƙata shi ne hutu daga dukkan wani aikin ƙarfi. Hakan zai taimaka wajen cikin ya zauna ba tare da ya zube ba.
b. Cikin da yake zubar da jini sannan bakin mahaifa ya buɗe. Wannan cikin bai fiye zama ba.
c. Cikin da ya zube, amma kuma ya bar sauran guntattakin dattin cikin a mahaifa. Abin da wannan yake buƙata shi ne a yi hoton ciki a tabbatar da akwai sauran dattin, idan akwai sai a bayar da ƙwaya ta ‘Misoprostol’ ko kuma a yi wankin ciki, domin fitar da sauran dattin.
d. Cikin da ya zube gabaɗaya ba tare da ya bar guntu ba. Wannan ya riga ya zube, sai dai za a iya shan ƙwayoyin da suke bayar da kariya daga cutar Bakteriya (Antibiotics) da kuma masu ƙara jini (Haematinics).
e. Cikin da ya lalace sannan kuma bai zube ba yana nan a cikin mahaifa ya manne. Abin da wannan cikin yake buƙata shi ne a yi hoton ciki, bayan an yi an gano shi ɗin ne, sai a zo asibitin da suke da ingantattun kayan aiki a yi wankin ciki bayan an duba an tabbatar da bakin mahaifa a buɗe yake.
f. Cikin da ya zube sannan ya sa cuta a cikin mahaifa. Shi ma wannan a zo asibiti domin a gana da likitoci masana a fannin.
2. ɓarin da aka yi da gangan wanda aka riga aka shirya:
Shi ma a ƙasan shi akwai kashe-kashe kamar haka:
a. Zubar da ciki ta hanyar shan magani.
b. Zubar da ciki ta hanyar yin aiki irin su wankin ciki da kuma amfani da wasu ƙarafuna don a cire ciki.
Abubuwan da suke janyo zubewar ciki:
1. ɓarin ciki bisa tsautsayi:
Abubuwan da suke kawo haka sune kamar:
a. Cuta; misali zazzaɓin cizon sauro, ƙarancin jini, cuta mai karya garkuwar jiki, shan magungunan da ba likita ba ne ya rubuta.
b. Shekaru.
c. Jirkicewar ƙwayoyin halitta.
d. Ciwo a mahaifa.
2. ɓarin da aka yi da gangan:
Abubuwan da suke sawa a yi su ne kamar haka:
a. Cikin da aka same shi ba ta hanyar aure ba.
b. Fyaɗe.
c. Samun ciki a lokacin da ba a shirya ba.
d. Matan da suka jarraba tsarin iyali, amma suka kasa dacewa.
Matakan magani:
-Hoton ciki don tabbatar da shin akwai cikin, ko kuma a akwai sauran dattin cikin.
-Magani ko na ce ƙwaya idan cikin ya faɗi, amma ya bar saura.
-Wankin ciki.
-Magungunan da suke bayar da kariya daga kamuwa da cutar Bakteriya.
-Shawarwari ta fannin ilimi daga ƙwararru.
Abubuwan da ɓarin ciki yake haifarwa:
1. Zubar jini.
2. Ciwo a bakin mahaifa, musamman idan an yi wankin ciki ba a wajen da suke da kayan aiki masu kyau ba.
3. ƙwaƙwale mahaifa idan har wacce ba ƙwararriyar ma’aikaciya ba ce ta yi aikin (wankin ciki).
4. A wasu lokutan yana janyo matsalar rashin haihuwa.
Wasu ‘yan ƙananan shawarwari:
Yana da kyau a guji zubar da ciki ta hanyar da ba ta dace ba (Criminal Abortion).
Sannan a daina zuwa asibitocin da ba su da ingantattun kayan aiki su yi miki wankin ciki. Misali ƙananan asibiti (Primary Health Cares, Clinics).
Sannan a guji zuwa wajen ma’aikatan jinyar da ba su da lasisin aiki ko kuma ba nurses (ma’aikatan jinya) ko midwife (ungozama) ko doctor (likita) ba.
Sannan a guji shan magunguna barkatai a lokacin da ake ɗauke da ƙaramin ciki.
Idan a na ɗauke da ƙaramin ciki a tabbatar duk wata jinya wajen likitan da ya shafi ɓangaren ciki aka je.
A guji shan itatuwa (ko jiƙe-jiƙe) barkatai a lokacin da ake da ciki.
©® Shamsiyya Usman Manga (Registered Midwife)
