Ɗan Atiku ya mayar wa ɗan gwamnan Bauchi zazzafan martani

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Muhammad Atiku wanda ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa ne, ya ce, gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, bai taɓa mara wa mahaifinsa baya ba a zaɓukan 2019 da 2023 da aka yi.

Ɗan Atiku na wannan kalamai ne a matsayin martani ga ɗan gwamnan Bauchi, Shamsu Bala wanda ya zargi ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa da yi wa mahaifinsa maƙarƙashiya a zaɓen 2023.

A ranar Asabar ce, Shamsu ya ce Atiku ba ma ya tunanin zuwa ya nemi gafarar mahaifinsa duk kuwa da shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027 da yake yi.

“Bambancin da ake akwai yanzu shi ne Shamsu ya fito fili ya nuna mana cewa ka da mu sa ran samun goyon mahaifinsa (gwamnan Bauchi),” ya faɗa.

Ɗan Atiku Abubakar ya yi wannan martanin ne cikin wani saƙo da ya aiko wa da Manhaja a ranar Litinin, yana mai jaddada cewa gwamnan Bauchi ne ya yi wa mahifinsa zagon ƙasa a zaɓen 2023.

A cewar jawabin da ya aiko mana wanda ɗan Atikun ya sanya wa hannu, ya ce, ba komai a kalaman ɗan gwamnan Bauchin face girman kai da nuna su wasu tsiya.

“Idan Shamsu ba ya bibiyar labarai, bari na tuna masa yadda maigidan mahaifinsa a siyasa, ministan Abuja, Nysome Wike, ya bayyana yadda gwamnan Bauchi ya shirya kutunguilar ganin Atiku ya faɗi a zaɓen 2023.

“Yana da kyau na faɗi cewa, burin da gwamna Bala Mohammed ke da shi na son tsayawa takarar shugaban ƙasa, shi ne babban abin da ya sa ya gaza tafi da ƙungiyar gwamnonin PDP yadda ya kamata da kuma samun girmamawar da ta dace. Kuma muna da sanin cewa yana yin wata ƙulla-ƙulla ga gwamnatin Tinubu,” a cewar ɗan Atiku Abubakar.

A cikin wani rubutu da ya wallafa a dandalin sada zumunta, Shamsu ya zargi Atiku da mara wa Air Marshal Abubakar Sadiƙ (ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen 2023) baya. Sannan ya ce Atikun ya yi amfani da wasu dattawan jihar Bauchi domin ya yaƙi mahaifisa wanda “da ƙyar muka sha.”

Akwai wani da ake cewa Kirfi wanda tsohon ministan harkokin waje ne a lokacin Shagari kuma ministan ayyuka na musamman a lokacin Obasanjo wanda kuma abokin siyasar Atiku ne da ake ganin yana daga cikin dattawan da Atikun ya yi amfani da su wajen yaƙar gwamnan Bauchin don kar ya sake komawa kujerarsa ta gwamna.

Sai kuma babban jigo a jam’iyyar PDP wanda tsohon kakakin majalisar dattawa ne Yakubu Dogara, wanda ake ganin shi ma ya yi wa Atiku aiki a wancan lokaci.

Duk da tsamin dangantakar Atiku da Bala Muhammad, ɗan takarar PDP ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa da sama da ƙuri’u 100,000 sama da Shugaba Bola Tinubu na APC.

Kalaman Shamsu da suka jawo wannan martani sun zo ne bayan Atiku Abubakar ya kai wa tsohon Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ziyara a Kaduna wanda masana siyasa ke ganin wani yunƙuri ne na ƙulla maja domin kawar da APC a zaɓen 2027.

Sai dai a shekarar 2022, gwamna Bala ya ƙalubalanci Atiku da sauran ‘yan takarar a zaɓen cikin gida na fidda ɗan takarar Shugaban ƙasa wanda daga baya ya nemi tazarce a 2023.

Ana ganin har yanzu gwamna Bala muhammad na da ra’ayin sake tsayawa takara domin karawa da Atiku a zaɓen fidda gwani na PDP a 2027 kasancewarsa Shugaban ƙungiyar Gwamnonin PDP wanda ake ganin zai sa ya yi ƙarfi sosai da sosai.

By ukarofi