Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
A ranar Talata, 1 ga watan Afrilu, 2025, masarautar Bazhi da ke Gundumar Tuna cikin ƙaramar Hukumar Gurara a Jihar Neja, ta yi sabbin naɗe-naɗe domin cigaban yankin.
Naɗe-naɗen sun haɗa da masu unguwanni huɗu da fadawa 20.
Tun farko sai da aka bai wa babban Limamin Bazhi, Sheikh Salihu Muhammad, zarafin buɗe taro da addu’a kafin daga bisani Hakimin Tuna, Malam Yusuf Shaban ya gabatar da jawabin maraba.
A nasa ɓangaren, Dagacin Bazhi, Malam Yahaya Umar ya bayyana cewa, sun yi naɗe-naɗen bisa cancanta domin kuma domin cigaban yankin.
Masu unguwannin da aka naɗa su ne: Mohammed Ibrahim, Mai Anguwan Paitapi; Sani Salihu, Mai Anguwan ɓulla; sai kuma Kabiru Mohammed wanda aka naɗa a matsayin Mai Anguwan Yadna.
A ɓangaren fadawa kuwa, akwai Salihu Male, Sarkin Fada; Adamu Umar, Magajin Bazhi; Mohammed Darato, Zagwai Bazhi; Mohammed Umar, Makun Bazhi; Shuaibu Umar, ɗandami Bazhi.
Yahaya Yakubu, Padakai Bazhi; Ismaila Yusuf, Wakilin Bazhi; Mohammed Shuaibu, Sarkin Samari Bazhi; Adamu Hussaini, Barde; Abdullahi Sadiƙ, Bakaci; Musa Umar, Makama.
Saidu Yakubu, Jami; Abdullahi Mohammed, Nagenu; Mohammed Yakubu, Sarkin Baka; Audu Yakubu, Lupka; Aliyu Ibrahim, Dagbeji; Mohammed Kasuwa, Marafa; Mal. Haruna Mohammed, Sanboki; sannan Adamu Mohammed, a matsayin Ubandoma.
Da yake jawabi a madadin waɗanda naɗe-naɗen ya shafa, Mal. Adamu Umar (Magajin Bazhi), ya yaba da damar da aka ba su don yi wa yankinsu hidima, tare da ba da tabbacin za su yi bakin ƙoƙarinsu wajen sauke nauyin da aka ɗora musu.
Taron ya samu mahalarta na kusa da nesa, kuma ya gudana cikin salama ya watse cikin aminci.
