‘Ɗan jarida ya maka ‘yan sandan Abuja da wasu a kotu bisa zargin ƙwacen fili

Spread the love

Daga USMAN KAROFI a Abuja

Wani ɗan jarida mai zama a birnin tarayya Abuja, Abdussalam Ibrahim Ahmad, ya shigar da ƙara gaban kotu yana zargin ‘yan sanda da wasu mutane da yunƙurin ƙwace masa filinsa dake garin Dakwa, a ƙaramar hukumar Tafa ta Jihar Neja. A cikin ƙarar da aka shigar a kotun ƙoli ta Jihar Neja da ke Suleja, an ambaci wani dillalin gida mai suna Muhammad Tukur a matsayin wanda ya kutsa cikin filin da ake gardama a kai.

Ahmad ya bayyana cewa ya sayi filin ne tun shekarar 2018 tare da cikakken takardar mallaka daga hukumar ƙaramar hukumar Tafa. Sai dai kusan shekaru biyar da suka wuce, Tukur ya bayyana yana ikirarin mallakar filin tun sama da shekaru ashirin, yana kuma buƙatar Ahmad ya dakatar da duk wani aiki na gine-gine a wajen.

A cikin ƙarar da lauya Douglas Najime ya shigar a madadin ɗan jaridar, ana neman kotu ta hana ‘yan sanda, Sufeto Janar na ‘yan sanda, kwamandan yankin Kubwa, da kuma Ministan Shari’a tsoma baki ko barazana da kama Ahmad dangane da wannan rikicin mallakar fili mai lamba 24, bulok C, mai girman murabba’in mita 531.5. Haka kuma Ahmad yana neman diyya ta naira miliyan 50 kan abin da ya bayyana a matsayin kamu ba bisa ƙa’ida ba, cin mutunci, barazana da tsangwama.

Baya ga hukumar ‘yan sanda, an haɗa da wasu mutane huɗu a cikin ƙarar: Abu Ango, Blessing Iliya, Muhammad Tukur da Faruk Ɗahiru. Har zuwa yanzu, babu ɗaya daga cikin waɗanda ake ƙarar da ya mayar da martani ko halartar zaman kotu, duk da cewa an miƙa musu takardun gayyata.

Rahotanni sun nuna cewa ana fama da rikice-rikice da dama na mallakar filaye a unguwar Dakwa, wanda galibinsu ke biyo bayan yawan baiwa mutane filaye guda daga hukumomi daban-daban.

By ukarofi